Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya bi sahun sauran shugabannin Afirka 49 zuwa birnin Washington D.C. domin halartar taron Amurka da shugabannin Afirka, wanda za a fara yau Talata, 13 ga watan Disamba.
Croatia ta ce, ba za ta yi yunkurin mai da hankali kan dan wasan Argentina Lionel Messi shi kadai ba, amma a maimakon haka za ta mayar da hankali wajen hana daukacin 'yan wasan baki dayansu a wasan daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin duniya ranar Talata.
A cigaba da yakin neman zaben sabon shugaban Najeriya a ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da magoya bayan su na bayanan abubuwan da a ke ganin za su haddasa mu su cikas.
Shugaba Joe Biden na shirin karbar bakuncin shugabannin Afirka da dama a Washington a wannan makon a daidai lokacin da fadar White House ke neman takaita gibin amincewa da Afirka.
Hukumar Tattara Kudaden Gwamnati da Kula da yadda ake kasafta su ta sha alwashin daukan kwararran matakai akan ma'aikatu da hukumomin gwamnati da ba sa kai kudade asusun gwamnati na bai daya.
Majalisar Dattawa ta amince da wani kudurin doka da zai bada dama a kafa wata hukuma ta musamman da za ta rinka kula da shirin nan na inganta rayuwar al'umma da kawar da talauci.
A cikin shirin na wannan makon, masana a Najeriya sun fara tsokaci a game da sabon tsarin da gwamnati ta sanar na koyar da daliban firamare da harshen uwa, a maimakon turanci.
Yadda Cutar Dajin Gaban Namiji Ko Kuma Prostrate Cancer A Turance Ke Shafar Maza A Nahiyar Afrika
Wani kwamitin bincike na mutum 7 da shugaba Buhari ya kafa a asirce don duba ayyukan tara kudaden shiga na yau da kullum na bankuna, ya gano zunzurutun kudi da su ka kai dala biliyan 171 da babban bankin Najeriya ya ajiye a wani asusun da baya amfanar gwamnati.
Amurka za ta karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka 49 da kuma tawagar kungiyar Tarayyar Afirka a birnin Washington domin halartar taron kwanaki uku na Amurka da Afirka da za a fara ranar Laraba mai zuwa.
Kasar Qatar ta kaddamar da bincike kan mutuwar wani dan kasar Philippines biyo bayan rahotannin da ke cewa, mutumin ya mutu ne a wani wurin horo a lokacin gasar cin kofin duniya.
An fara taron bita da karawa juna sani na yini uku a Kano, ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an Hisbah na jihohi 6 dake arewa maso yammacin Najeriya da nufin neman dabaru da hikimar tunkarar kalubalen zamantakewar gida da cin zarafin mata da kananan yara.
Shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru kuma tsohon dan wasan kwallon kafa Samuel Eto’o ya nemi afuwar wani mutum da ya ture kasa a wani abin da ya kira ‘mummunar hatsaniya’ a wajen wani filin wasa na gasar cin kofin duniya da safiyar Talata.
A jamhuriyar Nijer wani harin ta’addanci da aka kai a tashar bincike ta ‘yan sandan garin Say dake a km 60 da birnin Yamai ya haddasa asarar rayukan da suka hada da jami’an tsaro da farar hula.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto wasu mutane hudu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga wani masallaci da yammacin ranar Asabar, kuma suna neman wasu akalla 13 da suka bace.
Gwamnatin Najeriya tace tana samun galaba wajen yaki da ‘yan ta'adda har tana kusa da buda sashen kula da sauka da tashin Jiragen sama na rundunar sojin kasa.
Daga dukan alamu tsuguno ba ta kare ba akan kiraye kiraye da kungiyoyi masu zaman kansu ke yi a Najeriya cewa Babban Alkalin Alkalan Kasar, Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya ajiye aikin sa bayan da ake zargin ya karya ka'idar shari'a.
Hukumar gidajen gyara hali ta Najeriya ta kaddamar da wasu sauye sauye da a cewarta za su inganta ayyukan ma’aikatanta da rayuwar fursunoni da ake tsare da su a fadin kasar.
A wani mataki na dakile akidar yanayin siyasa, kwamitin tabbatar da zaman lafiya na jihar Kano da hadin gwiwa da hukumar NBC sun gudanar da taro na musamman da shugabannin kafofin labaru da kuma wakilan manyan kafofin labarai na cikin gida da na ketare wadanda ke aikin tura rahotannin daga Kano.
Domin Kari