An dai sanya ido sosai kan yadda Qatar ke mu'amala da ma'aikatan bakin haure yayin da ake shirye-shiryen tunkarar gasar, inda kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka zargi kasar da cin zarafin ma'aikata -- zargin da gwamnati ta yi watsi da su.
Nasser Al Khater, shugaban zartarwa na gasar cin kofin duniya ta 2022 a Doha, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wani ma'aikaci ya mutu, amma bai bayar da wani karin bayani ba. Ya yi wa iyalansa ta’aziyya kuma ya kara da cewa “mutuwa wani bangare ne na rayuwa”.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Philippines ta fitar, ta tabbatar da cewa daya daga cikin 'yan kasar ya mutu a lokacin da yake aiki a wani wurin shakatawa da ke kudancin Doha babban birnin kasar. Ta ce ofishin jakadancinta yana "aiki tare da hukumomin shari'a don tabbatar da karin cikakkun bayanai game da mutuwarsa".
Jaridar wasanni ta yanar gizo "The Athletic", a ranar Laraba ta buga labarin cewa mutumin ya yi aiki ne da wani kamfani da ya yi kwangilar gyaran fitulu a wurin da ake ajiyar mota da ke Sealine Resort, wurin horon 'yan wasan kasar Saudiyya. An ce ya mutu ne bayan ya zame daga kan wani kangi yayin da yake amfani da wasu kayan aiki, ya buga kansa a kan siminti.
Hatsarin ya afku ne a lokacin gasar cin kofin duniya, amma ba a fayyace lokacin ba.
~ REUTERS