Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KATSINA: 'Yan Sanda Sun Kara Himma Wajen Neman Masu Ibada 13 Da Aka Sace A Masallaci


Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Katsina
Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Katsina

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto wasu mutane hudu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga wani masallaci da yammacin ranar Asabar, kuma suna neman wasu akalla 13 da suka bace.

A yau litinin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya ce masallatan da har yanzu ba a gansu ba, yawancin maza ne manya.

Ya ce wasu ‘yan bindiga ne a kan babura su ka kai hari a masallacin da ke Funtua, na tsawon kimanin sa’o’i shida a arewacin Abuja, a daren Asabar a lokacin da mutane ke Sallah. Maharan sun harbe Limamin da wani mutum guda.

Wasu mutane da su ka raunata
Wasu mutane da su ka raunata

Isah ya shaidawa Muryar Amurka cewa su biyun sun tsira kuma suna jinya a wani asibiti da ke yankin.

Lamarin ya faru ne yayin da masu ibada ke gudanar da sallarsu ta karshe na daren,” in ji shi, “Kafin isowar tawagar ‘yan sandanmu tuni ‘yan ta’addan suka tsere tare da wasu masu ibada. An ceto hudu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, yanzu haka muna neman masu ibada kusan 13.”

Kafofin yada labaran cikin gida sun ba da rahoton bacewar mutane fiye da 40.

Hare-haren sun kara matsin lamba ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta inganta tsaro gabanin zaben watan Fabrairu domin zaben wanda zai gaje shi.

XS
SM
MD
LG