Kungiyoyin na tuhumar sa ne bisa wani yabon gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da shiga wata kungiya ta gwamnan Jihar Ribas da ake kira Intergrity Group.
Akan haka ne gamayyar kungiyoyi masu fafutakan ganin a yi adalci a gudanar da Mulki reshen birnin tarrayya ke kira gare shi da ya ajiye aiki.
Babban Alkalin Alkalan Najeriya CJN Olukayode Ariwoola yana tsakiyar wata guguwa da ke kadawa da karfin gaske bayan da wasu ke ganin kaman ya karya ka'ida na aikin sa na shari'a.
A yayin da yake magana a wajen wata liyafa da shugaban gwamnonin G5 kuma Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike ya shirya, an ruwaito cewa Ariwoola ya nuna amincewar sa da kungiyar gwamnonin na G5, saboda haka ana ganin ya shiga sigar siyasa tsantsan kamar yadda mai magana da yawun kungiyoyin fafutukan tabbatar da adalci a gudanar da mulki Babanagari Suleiman ya yi tsokaci cewa a bayyane yake cewa Cif Joji ya ci amanar ka'idojin tsaka tsaki da duniya ta amince da shi yayin da yake bayyana ra'ayinsa game da kasancewar gwamnan jihar sa a cikin gwamnonin PDP da suka fusata.
Suleiman ya ce wannan abu ne da zai sa ba za a yarda da aikin sa ba, saboda haka ya sauka a nada wani.
Da yake amsa tambayar ko Cif Joji bashi da yancin fadin albarkacin bakinsa a matsayin sa na dan kasa, masanin shari'a Barista Mainasara Umar ya yi bayani cewa ana wa alkalai kallon dodanni, saboda doka ba ta amince masu yin mu'amala ba ko wace iri.
Kundin tsarin mulki kashi 203 ya ba su dama su shimfida ka'idojin aikin su ta yadda ba za su ci amanar kasa ba, domin za su iya sa wa a kama kowa komin girman mukamin sa, kuma suna iya sa wa a daure kowa, koma a iya kashe mutum, saboda haka abinda Alkalin Alkalan ya yi, babban kuskure ne.
Amma ga masanin a harkokin siyasar Kasa da Kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi bayani cewa lallai abinda Alkalin Alkalan ya yi ba daidai ba ne saboda za a ga kaman idan shari'ata zo gaban sa akan jama'an Nyesome Wike zai iya daga masu kafa.
Farouk ya ce kwananan kotun koli ta fito ta ce akwai kararraki da suka shafi siyasa sama da dubu 6. Farouk ya ce sai dai za yi masa rangwame domin kwanannan ya kama aiki kuma a nuna masa idan da wani abu a tsakanin su da gwamnonin bai kamata ya nuna ba.
Kashi 7 na kundin tsarin mulki Najeriya na 1999 kamar yadda aka gyara, na nuna cewa masu shari'a ba za su fito fili karara su bari sha'awarsu ta shafi aiyukan su na hukuma ba ko da a wani hali suke.
Saurari rahoton cikin sauti: