Kasar Croatia na neman zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniya karo na biyu a jere bayan da ta sha kashi a wasan cin kofin a 2018 da Faransa.
Sun bai wa Brazil mamaki a gasar wasan daf da na kusa da karshe bayan da ta zura kwallo a raga a cikin karin lokaci amma sai suka zura kwallo a ragar Brazil da bugun daga kai sai mai tsaron gida.
"Har yanzu ba mu da wani takamamman shiri na dakatar da Messi kuma yawanci ba ma mayar da hankali wajen dakatar da dan wasa daya shi kadai, sai dai daukacin kungiyar baki dayansu," in ji dan wasan gaban Bruno Petkovic a wani taron manema labarai jiya Lahadi.
"Za mu yi kokarin dakatar da su a kungiyance ba tare da nuna alamar mutum daya ba. ‘Yan wasan Argentina ba Messi kadai ba ne, suna da manyan 'yan wasa da dama, dole ne mu dakatar da dukan 'yan wasan Argentina."
Kawo yanzu Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai shi ne kan gaba a ‘yan wasan na Argentina, wadanda su ma suka bukaci bugun fanariti bayan da suka kasa zura kwallaye biyu a ragar Holland a wasan daf da na kusa da na karshe.