Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akufo-Addo Ya Halarci Taron Amurka Da Shugabannin Afirka A Washington


Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya bi sahun sauran shugabannin Afirka 49 zuwa birnin Washington D.C. domin halartar taron Amurka da shugabannin Afirka, wanda za a fara yau Talata, 13 ga watan Disamba.

Taron wanda shugaban kasar Amurka Joe Biden zai jagoranta, zai sabunta dangantakar Amurka da Afirka, da inganta hadin gwiwa kan muhimman batutuwan da suka shafi duniya baki daya.

Shugaba Akufo-Addo ya samu rakiyar uwargidansa, Rebecca Akufo-Addo; Ministar Harkokin Waje, Shirley Ayorkor Botchey; Ministan ciniki, Alan Kwadwo Kyerematen; Ministan Ayyuka da Gidaje, Francis Asenso Boakye; Ministan Muhalli, Kimiyya da fasaha da Ƙirkire-kirkire, Dokta Kwaku Afriyie; da wasu jami'ai a fadar shugaban kasa da ma'aikatar harkokin waje.

Masani a kan hulda tsakanin kasa da kasa da harkokin tsaro, Irbad Ibrahim, ya gayawa Muryar Amurka cewa wannan taro na da muhimmanci ga Amurka da kuma Afirka.

Ya ce, kasashen Rasha da China sun karfafa dangantaka da Afirka, domin haka ita ma ya kamata ta farfado da tsohuwar alakarta da Afirka. Haka kuma ya kara da cewa, Afirka ta bude sabon babi da za ta samu tallafi daga Amurka, kuma amfanin ya kasance ya tsaya a nan Afirka.

Mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum, Malam Isa Mairago Gibril Abbas ya ce lallai wannan taro zai bunkasa cinikayya da diflomasiya da dimokradiya ga Ghana da Afirka baki daya.

Kasar Amurka da wasu kasashen Afirka na da alaka mai karfi a bangarorin diflomasiya, tattalin arziki, tsaro da sauransu.

Yunus Salahudeen Wakpenjo, manazarci kan al’amuran yau da kullum ya ce, duk abinda ya gani na ci gaba a kasar Amurka, ya zo da su Ghana kuma ya kwatanta aikata hakan.

Shugaba Akufo-Addo zai dawo Ghana a ranar Asabar, 17 ga Disamba, 2022, kuma mataimakin shugaban kasa, Dr. Mahamudu Bawumia, zai yi aiki a madadinsa kamar yadda dokar kasa, sashe na 60 (8) ta tanadar.

Saurari rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG