Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hisbah Na Fama Da Kalubalen Warware Matsalolin Mata Da Yara-Rano


Taron Hisbah
Taron Hisbah

An fara taron bita da karawa juna sani na yini uku a Kano, ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an Hisbah na jihohi 6 dake arewa maso yammacin Najeriya da nufin neman dabaru da hikimar tunkarar kalubalen zamantakewar gida da cin zarafin mata da kananan yara.

Cibiyar bunkasawa, nazari da ayyuka DRPC mai bincike kan kyautata ala’amuran Jama’a, tare da hadin gwiwa da gidauniyar Ford Foundation, da kuma tallafin kungiyar mata ta FOMWAN ne suka shirya taron da ya samu mahalarta daga jihohin Jigawa, Katsina, Sokoto, Kebbi da kuma Zamfara.

Taron Hisbah
Taron Hisbah

Malam Ubale Ibrahim Rano, babban Jami’i mai kula da ayyukan ofishin cibiyar a jihar Kano yace cibiyar a kowane lokaci na da sha’awar hanyoyin inganta kiwon lafiya mata da yara da kuma sha’anin zamantakewar su, kuma ta lura da yadda hukumomin Hizbah ke fama da kalubalen warware matsalolin mata da yara masu nasaba da zamantakewar aure, don haka take kokarin tallafa musu da dabaru da hikimomin tunkarar wannan kalubale.

Taron Hisbah
Taron Hisbah

Farfesa Usman shu’aibu na sashin koyar da shari’ar Musulunci a tsangayar koyar da aikin lauya ta Jami’ar Bayero Kano ya gabatar da makala data maida hankali akan cin zarafin mata ta mahangar shari’ar Musulunci. Yace akwai banbance-banbance tsakanin mahangar shari’ar Musulunci da kuma mahangar masu rajin kare hakkin mata na wannan zamani akan wasu batutuwa da suka shafi cin zarafin mata, inda shari’ar musulunci ke kallon wasu batutuwan a matsayin hukunci, masu rajin kare hakkin mata na ganin hakan a matsayin cin zarafi.

Taron Hisbah
Taron Hisbah

Malam Umma Umar jagorar kungiyar kare hakkin mata da yara ta Mar’atussaliha a jihar Kebbi ta ce aikace-aikacen su ya kara nuna yadda mata da yara ke fuskantar kalubale a sassan jihar.

A karshen taron ana sa ran kwamandojin Hisbah a jihohin 6 a yankin arewa maso yammacin Najeriya zasu ilimanta da sabbin dabarun wadannan kalubale da suka dabaibaye rayuwar mata da yara a yankunan su.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
XS
SM
MD
LG