Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NBC Ta Nemi Tallafin ‘Yan Jarida Don Fadakar Da Jama’a Game Da Zabe Cikin Lumana


Taron kwamitin tabbatar da zaman lafiya na jihar Kano hadin gwiwa da hukumar kula da kafofin labarai na Radio da talabijin ta Najeriya wato NBC
Taron kwamitin tabbatar da zaman lafiya na jihar Kano hadin gwiwa da hukumar kula da kafofin labarai na Radio da talabijin ta Najeriya wato NBC

A wani mataki na dakile akidar yanayin siyasa, kwamitin tabbatar da zaman lafiya na jihar Kano da hadin gwiwa da hukumar NBC sun gudanar da taro na musamman da shugabannin kafofin labaru da kuma wakilan manyan kafofin labarai na cikin gida da na ketare wadanda ke aikin tura rahotannin daga Kano.

Jan hankalin kafofin labarai game da hakkin da ke rataye a wuyansu na kaucewa yada kalaman tunzuri dake fitowa daga bakin ‘yan siyasa da nuna kwarewa wajen aikin jarida kana da bi sau da kafa dokoki da ka’idojin yada labarai na hukumar NBC mai kula da kafofin talabijin na cikin muhimman batutuwan da mahalarta taron sukayi mahawara akai.

Malam Adamu Salisu dake zaman babban Jami’in ofishin Kano na hukumar ta NBC wanda ya yi tsokaci game da daftarin kundin ka’idojin aikin jarida na hukumar, yace duk bayan shekaru 4 -5 ana sabunta wannan daftari domin yayi dai-dai da yanayin da ake ciki.

Taron NBC
Taron NBC

Sai dai ya zargi ma’aikatan yada labarai na Radio da talabijin a Najeriya da rashin kiyaye ka’idojin dake kunshe a cikin daftarin yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Sai dai Alhaji Aliyu Umar Harazimi, Dan Amar na Kano, wanda ya wakilci shugaban kwamitin zaman lafiya na Kano Farfesa Ibrahim Umar yace kwaitin ya lura da amincin dake tsakanin al’umar gari da ‘yan jarida da kuma muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a cikin jama’a.

Yace hakan ta sanya kwamitin ya shirya wannan taro domin neman tallafin ‘yan jarida ta yadda za’a fadakar da Jama’a game da muhimmancin yin zabe cikin kwanciyar hankali da salama.

Shi kuwa, kakakin hukumar zabe a jihar Kano Ahmad Maulud Adam ya fayyace wasu daga cikin sauye-sauyen da hukumar tayi a kudin zabe kuma ya bukaci jami’an kafofin labarai su maida hankali sosai akan su. Yana mai cewa, sabuwar naurar zabe ta BVAS zata rinka tantance fuska da hannun mai kada kuri’a kuma itace ta maye gurbin na’urar da aka yi amfani da ita ta Card Reader.

Masu kula da lamura dai na ganin kalaman tunzura magoya baya da suka fito daga bakin shugabannin reshen jihar Kano na jam’iyyun APC da NNPP a baya bayan nan, sun kara zaburar da masu ruwa da tsaki a Kano su dauki matakan tabbatar da zabe ya gudana cikin lumana a jihar.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG