Kasashen biyu dama sun dade da jure hamayya ta tsawon shekara guda, saboda su ne ke da masana'antun nishaɗi mafiya girma a Afirka, kuma kusan su ne mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar.
Fitattun mawakan Najeriya da suka hada da Burna Boy, Davido, Tems, Ayra Starr, Olamide, da Asake, basu yi nasara ba a Kyautar Grammy ta 2024.
A jiya litinin masarautar Buckingham ta bayyana cewa, Sarki Charles na 3 ya kamu da cutar sankara kuma tuni ya fara karbar magani, duk da dai masarautar bata bayyana ko wacce irin sankara sabon Sarkin Ingilan ya kamu da ita ba.
Akalla mata 35 ne suka bace bayan da masu garkuwa da mutane suka kama wadansu mata da suka dawo daga wani daurin aure a arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jami’ai suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a Litinin din nan.
Hukumar wasan kwallon kafa ta duniya ta FIFA, ta sanar ranar Lahadi cewa za a buga wasan karshe na cin kofin duniya na shekarar 2026 a filin wasan Metlife da ke birnin New Jersey.
Wata takardar babban bankin kasar da wani jami’i a bankin ya tabbatar da sahihancinta ce ta bayyana sunayen bankunan da aka haramtawa amfani da dalar.
Gwamnatin Amurka ta yi tayin ba da tukuicin dala har miliyan 5 ga duk wanda ke da bayanan da za su sa a gano Abu Ali al-Tunisi ko kuma inda yake. Al-Tunisi jigo ne a kungiyar ta'addanci ta ISIS. Yana da rauni a hannunsa na dama da idon dama.
Kwana daya kafin a soma yakin neman zaben shugaban kasa a Senegal, shugaba Macky Sall ya sanar da dage zaben kasar saboda rikicin da ke faruwa tsakanin majalisar dokokin kasar da kotun tsarin mulki, a cewarsa.
Gamayyar kungiyoyin fararen hula sama da 40 sun kai karar Shugaban Najeriya Bola Tinubu, inda suka yi kira gare shi da ya magance matsalar rashin tsaro da ta kara kamari tun bayan hawansa mulki a watan Mayun da ya gabata.
Amurka ta sake nanata kudurinta na tsayawa tsayin daka a fannin tattalin arziki da kasuwanci a kasashen Afirka.
Isra'ila ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta yanke a makon da ya gabata, ta hanyar kashe daruruwan fararen hula a Gaza 'yan kwanaki bayan yanke hukumcin, kamar yadda Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta fada jiya Laraba,
Wani mutum da ake zargi da fille kan mahaifinsa a birnin Philadelphia, ya wallafa wani bidiyon mai ban tsoro a shafukan sada zumunta wanda ya nuna shi yana rike da kan da ya yanke yana kuma zagin gwamnati, kamar yadda hukumomi suka fada jiya Laraba.
Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya bayar da rahoton cewa, a ranar Laraba ne wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutumin da ya kashe mutum daya tare da jikkata wasu uku a wani hari da aka kai a birnin Seoul a bara.
An cafke wani mutum da ake nema kan laifin kashe budurwarsa tare da barin gawarta a wani wurin ajiye motoci a filin jirgin sama na Boston kafin ya tashi zuwa Kenya, kamar yadda ‘yan sandan Kenya suka bayyana a jiya Talata.
Wani mummunan karo tsakanin wata motar bas mai hawa biyu da wata babbar motar daukar kaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 tare da jikkata wasu 22 a ranar Talata a arewa maso yammacin kasar Mexico, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya yi tsokaci a game da tasirin sashin Hausa na Muryar Amurka.
A ci gaba da shagulgulan cikar VOA Hausa shekara 45 da kafuwa, ma’aikatan shashin a Washinton DC sun gudanar da ‘yar kwarya-kwaryar liyafa, wacce ta samu halartar baki daga Amurka da wakilan ofishin jakadancin Najeriya a Washington.
Domin Kari