Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Mahalarta Daurin Aure 35 a Najeriya


Yan bindiga
Yan bindiga

Akalla mata 35 ne suka bace bayan da masu garkuwa da mutane suka kama wadansu mata da suka dawo daga wani daurin aure a arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jami’ai suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a Litinin din nan.

Satar jama'a da aka yi a jihar Katsina shi ne mafi girma a cikin jerin sace-sacen da aka yi a baya-bayan nan a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Abubakar Aliyu ya ce ‘yan bindiga sun yi kwanton bauna ne tare da yin garkuwa da mata kimanin 35 da suke dawowa daga daurin auren a unguwar Sabuwa a daren ranar Alhamis.

Wasu da aka sace 'yan uwansu
Wasu da aka sace 'yan uwansu

Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Nasiru Muaz ya bayar da adadin da ya fi haka, inda ya ce sama da mutane 50 ne aka kama a hanyar komawa kauyen Damari bayan sun raka amarya gidan ango.

"Jami'ai sun ziyarci kauyen kuma an gaya musu cewa an dauke mutane 53," in ji shi.

Yana da matukar hadari ga ayarin motocin da ke dauke da amarya da kawayenta su fita kai amarya cikin duhu a cikin irin wannan wurin da ke fama da aika-aikan ‘yan fashin yayin da suke kuma waka.

Kwamishinan ya bukaci mazauna yankin da su guji yin tafiye-tafiye da dare sannan ya ce jami’an tsaro na kokarin ganowa da kubutar da mutanen da aka kama.

Satar mutane don neman kudin fansa babbar matsala ce a Najeriya, inda kungiyoyin masu aikata laifuka ke kai hari kan manyan tituna, gidaje, har ma da sace yara a makarantu.

A farkon shekarar nan ne wasu masu aikata laifuka suka sace wasu ‘yan mata mata biyar a kusa da babban birnin tarayya Abuja, inda suka kashe daya bayan da wa’adin kudin fansa ya cika, lamarin da ya janyo cece-kuce a kasar.

A makon da ya gabata ne wasu masu garkuwa da mutane suka kai hari kan wata motar bas a Najeriya tare da sace yara biyar da malamansu a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar.

An kuma kashe wasu sarakunan gargajiya biyu a wani hari na daban a jihar a ranar Litinin da ta gabata, yayin da wasu ‘yan bindiga suka harbe wani sarkin gargajiya tare da yin garkuwa da matarsa a jihar Kwara a ranar Alhamis.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau karagar mulki a bara yana mai alkawarin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Wani Kamfanin tuntuba mai zamana kansa da ke bada rahotannin harkokin tsaro SBM Intelligence ya ce bisa ga rahoton da ya tattara, mutane 3,964 aka sace a Najeriya tun lokacin da Tinubu ya hau mulki a watan Mayu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG