Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ce Trump Bai Da Kariya Daga Tuhumar Saba Dokokin Zabe


Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump a kotu
Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump a kotu

Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ba shi da kariya daga gurfana gaban kuliya kan tuhume tuhumen nan na cewa ya yi amfani da hanyar da ta saba doka wajen yinkurin sauya faduwa zaben 2020 da ya yi don ya ci gaba da kasancewa bisa gadon mulki, hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke kenan jiya Talata a birnin Washington.

Hukuncin, wanda duka alkalai uku da ke shari’ar su ka zartas, ya yi watsi da ikirarin Trump na cewa lauya na musamman Jack Smith bai da hurumin tuhumar shi kan ayyukan da ya yi a kwanakin karshe na shugabancinsa ba, na sauya kayen da ya sha a hannun Joe Biden na Demokarat saboda suna da alaka da aikinsa na shugaban kasa a hukumance.

U.S. President Biden
U.S. President Biden

"Tsohon shugaba Trump shi ma ya zama dan kasa kamar ko wani dan kasa, tare da duk wani kariya na duk wani wanda ake tuhuma," in ji kotun. "Amma duk wata kariya na shugaba mai zartarwa da ya samu yayin da yake shugabancin kasa, daga sannan ba za ta iya kare shi daga wannan tuhumar ba."

A cikin tuhume-tuhume guda hudu, Smith ya zargi Trump da yin amfani da ikirarin karya cewa an yi magudin zabe don ya tursasa jami’an zaben jihohi, ma’aikatar shari’a da mataimakinsa Mike Pence, su hana majalisar ba da shaidar sakamakon zaben da ke nuna cewa ya sha kaye.

Trump, wanda shi ne shugaban kasa na farko da ake zargi da aikata manyan laifuka, ya musanta aikata ba daidai ba a shari’ar zargin magudin zabe, da kuma wasu tuhume-tuhume guda uku da ya ke fuskanta wadanda suka sa adadin tuhume-tuhume ya kai 91.

Kakakin yakin neman zaben Trump, Steven Cheung, ya ce hukuncin kotun daukaka kara "yana barazana ga ginshikin Jamhuriyarmu. Idan babu cikakken kariya, shugaban Amurka ba zai iya yin aiki yadda ya kamata ba!"

Hukuncin na ranar Talata, wanda Trump ya ce zai daukaka kara a kai, au zuwa babban kotun daukaka kara kuma kotun kolin Amurka, ya zo ne kusan wata guda bayan da alkalan daukaka kara uku suka saurari muhawara kan karar, tare da Trump a dakin shari’a.

Yayin da yake jiran hukuncin kotun daukaka kara, Trump ya yi ikirarin sau da dama a tarukan yakin neman zabe da kuma a shafukan sada zumunta cewa dukkan shugabannin Amurka na bukatar cikakken kariya daga tuhuma, domin kada abokan hamayyarsu na siyasa su tuhume su da laifuka da zarar wa'adin shugabancinsu na shekaru hudu ya kare.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG