Hukumomin Najeriya a jiya Talata sun yi kira da a yi taka-tsan-tsan kan abin da suka bayyana a matsayin "barazana" ga 'yan kasarsu da ke zaune a Afirka ta Kudu gabanin haduwar kasashen biyu a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka - wasan kwallon kafa da ke sabunta takun saka.
Kasashen biyu dama sun dade da jure hamayya ta tsawon shekara guda, saboda su ne ke da masana'antun nishaɗi mafiya girma a Afirka, a maimakon don su na mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar.
Sai dai a yanzu zaman dar dar na karuwa a fagen wasan kwallon kafa yayin da Najeriya da Afirka ta Kudu ke shirin buga wasan kusa da na karshe a Ivory Coast ranar Laraba.
Babban Ofishin Diflomasiyyar Najeriya a Afirka ta Kudu ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa 'yan Afirka ta Kudu na yin kalamai masu tayar da hankali a yanar gizo wadanda akasarinsu "sun kunshi barazana" ga 'yan Najeriya.
Ofishin harkokin diflomasiyya din ya bukaci ‘yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu da su kula da kalamansu, su lura da inda za su je kallon wasan... kuma su guji shiga cikin hayaniya, tarzoma ko tada hankali idan Super Eagles (laƙabin tawagar 'yan wasan kwalon Najeriya) suka lashe wasan kusa da na karshen.”
Sashen hulda da kasa da kasa na Afirka ta Kudu ya ce kasar "ba ta amince da fargabar da aka bayyana ba" a cikin sanarwar, in da ta kara da cewa: "Shawarar abin takaici ne saboda da alama ta haifar da zaman dar dar tsakanin 'yan kasar Afirka ta Kudu da 'yan Najeriya mazauna kasar ko kuma bakin da su ka zo ziyarar Afirka ta Kudu."
A cikin 2019, tashin hankali mai nasaba da kyamar baki a Afirka ta Kudu ya yi sanadin mutuwar mutane 12.
Najeriya da Afirka ta Kudu za su sake haduwa ne a wasan kusa da na karshe kamar yadda suka hadu a shekarar 2000, inda Najeriya ta ci da 2-0. Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a karo na uku a shekarar 2013, yayin da Afirka ta Kudu ta samu nasara a shekarar 1996.
Dandalin Mu Tattauna