Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TARON SHUGABANNIN AMURKA DA AFIRKA: Amurka Ta Aiwatar Da Yarjejeniyo 547, Da Kashe Dala Biliyan 14.2 A Shekarar 2023  - LeBlanc


Julie LeBlanc
Julie LeBlanc

Amurka ta sake nanata kudurinta na tsayawa tsayin daka a fannin tattalin arziki da kasuwanci a kasashen Afirka.

Da take jawabi jiya a wajen taron kasuwanci da zuba jarin Afrika da aka gudanar a cibiyar taron Eko dake jihar Legas, mai baiwa Amurka shawara kan harkokin kasuwanci Julie LeBlanc, ta ce a shekarar da ta gabata kadai, Amurka ta tallafa tare da kammala wasu sabbin yarjejeniyoyin guda 547, wadanda suka kai kimanin dala biliyan 14.2, wanda ke nuna karuwar kashi 60 cikin 100 na adadin da kuma darajar yarjejeniyoyi da aka cimma idan aka kwatanta da shekarar 2022.

LeBlanc ta ce, ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai kasashem yammacin Afirka ciki har da Najeriya, Cape Verde, Cote d'Ivoire, da Angola, ya nuna aniyar kudurin da Amurka ta dauka kan Afirka kwanan nan.

Blinken a Legas
Blinken a Legas

“Wannan ziyarar ta karfafa himmarmu wajen inganta hadin gwiwar tsaro, ayyukan kiwon lafiya, da bunkasar tattalin arziki a yankin."

“Gudunmawar da gwamnatin Amurka ta bayar na dala miliyan 160 don tallafawa cinikayya a Nahiyar Afirka ya misalta kudurinmu. Manufarmu wannan tallafin, ita ce faɗaɗa cinikayya da kuma tallafawa Mata da Matasa a Nahiyar Afirka."

LeBlanc ta cigaba da cewa: “Najeriya tana daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a Nahiyar, mun fahimci muhimmiyar rawar da take takawa a kasuwannin yanki da na duniya. Najeriya ta kasance babbar abokiyar cinikayyarmu ta biyu a Afirka."

“Muna ganin Nijeriya a matsayin babbar shugaba a Nahiyar, kuma babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da kyawawan dabi’unmu. Abin da ya amfanar da Nijeriya, zai amfanar da Afirka, da ma duniya baki daya.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG