Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar New York Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya Na 2026


Filin wasan Metlife da ke birnin New Jersey.
Filin wasan Metlife da ke birnin New Jersey.

Hukumar wasan kwallon kafa ta duniya ta FIFA, ta sanar ranar Lahadi cewa za a buga wasan karshe na cin kofin duniya na shekarar 2026 a filin wasan Metlife da ke birnin New Jersey.

Za a fara wasan ne da taka leda a shahararren filin wasa na Azteca dake babban birnin Mexico a ranar 11 ga watan Yuni.

A biranen Atlanta da Dallas zasu karbi bakuncin wasannin kusa da karshe, yayin da za a buga wasa a mataki na 3 a birnin Miami.

Sai wasannin quarter-final da za a buga a biranen Los Angeles, Kansas, Miami da Boston.

Jimlar birane 16 a fadin kasashen 3 za su dauki bakuncin wasannin, yayin da mafi yawa daga cikin wasannin za a yi su ne a cikin Amurka.

A baya an buga gasar cin kofin duniya na shekarar 1994 a Amurka inda aka yi wasan karshe a Rose Bowl da ke Pasadena, a kusa da Los Angeles.

An sanar da matakin ne ta wani shirin talabijin da aka watsa a Amurka ta arewa wanda ya nuna shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino tare da dan wasan barkwancin nan kuma dan wasan fina-finan hollywood Kevin Hart, da mawaki Drake, da kuma Kim Kardashian.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG