Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Da Masu Zanga-Zanga Sun Yi Arangama A Dakar Bayan Da Aka Dage Zaben Kasar


Magoya bayan jam'iyyar adawa a Senegal
Magoya bayan jam'iyyar adawa a Senegal

Kwana daya kafin a soma yakin neman zaben shugaban kasa a Senegal, shugaba Macky Sall ya sanar da dage zaben kasar saboda rikicin da ke faruwa tsakanin majalisar dokokin kasar da kotun tsarin mulki, a cewarsa.

Magoya bayan jam'iyyar adawa sun yi arangama da ‘yan sanda a Dakar babban birnin kasar Senegal a ranar Lahadi, bayan da shugaba Macky Sall ya bayyana dage zaben shugaban kasar da aka shirya yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, har sai illama sha Allahu, lamarin da kasashen duniya suka bayyana damuwa akai.

Kwana daya kafin a soma yakin neman zabe, Macky Sall ya jefa kasar cikin halin rashin tabbas, inda yace yayi hakan ne saboda rikicin da ke tsakanin majalisar dokokin kasar da kotun tsarin mulki akan kin amincewa da 'yan takara.

Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall

‘Yan majalisar dokokin kasar na gudanar da bincike kan wasu alkalan kotun tsarin mulki biyu, wanda ake jefa ayar tambaya akan cancantar su a shirye shiryen gudanar da zaben kasar.

“Zan bude teburin shawarwari a matakin kasa, wanda zai tattaro dukkan sharudan tabbatar da an yi zaben gaskiya da adalci wanda zai tafi da kowa,” in ji Sall, ba tare da ya bayyana sabuwar ranar zabe ba.

Bisa kiraye-kirayen da wasu 'yan takarar jam'iyyun adawa suka yi, daruruwan maza da mata masu shekaru dabam-daban, dauke da tutar Senegal wasu kuma sanye da rigunan 'yan wasan kwallon kafa na kasar, sun tattaru a wani shataletale da ke daya daga cikin manyan titunan babban birnin kasar da rana.

‘Yan sanda sun mayar da martani ga masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa, sannan suka bi su da gudu zuwa titunan da ke kusa, yayin da wasu masu zanga-zangar suka mayar da martani ta jifa da duwatsu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG