Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Kudu Ta Ce  Isra'ila Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Majalisar Dinkin Duniya Da Ta Hana Kashe-Kashe A Gaza


World Court rules on Gaza emergency measures in Israel genocide case, in The Hague
World Court rules on Gaza emergency measures in Israel genocide case, in The Hague

Isra'ila ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta yanke a makon da ya gabata, ta hanyar kashe daruruwan fararen hula a Gaza 'yan kwanaki bayan yanke hukumcin, kamar yadda Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta fada jiya Laraba,

Ministar ta ce kasarta ta nemi dalilin da ya sa ba a bada sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a karar da Afirka ta Kudu ta shigar a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba.

Ministan harkokin wajen kasar Naledi Pandor ta ce kasar Afirka ta Kudu za ta yi nazari kan gabatar da wasu matakai ta daban ga al'ummar duniya a wani yunkuri na hana Isra'ila kisan fararen hula a yakin da take yi da mayakan Hamas a Gaza, amma ba ta yi cikakken bayani ba.

Israel Palestinians
Israel Palestinians

Hukuncin farko da kotun kasa da kasa ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke a Afirka ta Kudu da ke zargin Isra’ila da kisan kiyashi a Gaza ya umurci Isra’ila da ta yi duk mai yiwuwa don hana mutuwa, halakawa da duk wani aikin kisan kiyashi ga Falasdinawa a yankin. Sai dai bai ba da umarnin tsagaita wuta ba. Ta kuma ce dole ne Isra'ila ta gaggauta kai agajin jinkai zuwa Gaza tare da gabatar da rahoto kan matakan da suka dauka na mutunta hukuncin cikin wata guda.

Tun bayan yanke hukuncin, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-haren soji, wanda ta ce tana kaiwa Hamas ne, an kuma kashe wasu daruruwan Falasdinawa, a cewar alkaluman ma'aikatar lafiya a Gaza da ke karkashin Hamas. Ma'aikatar ta fada jiya Laraba cewa, an kashe mutane 150 a yankin a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin Palasdinawa da suka mutu a yakin zuwa fiye da 26,700.

APTOPIX Israel Palestinians
APTOPIX Israel Palestinians

Kididdigar Ma'aikatar Lafiya ba ta bambanta tsakanin mayaka da farar hula ba. Ya ce akasarin wadanda suka mutu mata ne da kananan yara.

"Na yi imanin an yi watsi da hukunce-hukuncen kotun,” in ji ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu. “An kashe daruruwan mutane a cikin kwanaki uku ko hudu da suka gabata,kuma Isra'ila ta bayyana a fili cewa tana da ikon yin yadda ta ga dama."

Pandor ta ce akwai hatsarin idan har duniya ba za ta yi komai ba wajen hana farar hular da ake kashewa a Gaza, ta kuma ce rashin daukar mataki makamancin haka ya taimaka wajen mummunan kashe-kashen da aka yi a Rwanda a shekarar 1994, lokacin da aka kashe sama da mutane 800,000 a kasar da ke gabashin Afirka.

"Muna bari hakan ya sake faruwa, a gaban idanuwanmu, a kan talebijin mu," in ji Pandor.

Hukuncin kotun dai ya hau kan Isra'ila, kuma kasar za ta iya fuskantar takunkumin Majalisar Dinkin Duniya idan aka same ta da saba umarninta, duk da cewa kawarta Amurka na na iya hana ta fuskantar duk wani takunkumin.

Netanyahu ya ce Isra'ila "za ta ci gaba da yin abin da ya dace don kare kasarmu da kare mutanenmu." Isra'ila ta ce harin na da nufin rusa kungiyar Hamas bayan harin da ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,200, galibi fararen hula.

Isra'ila ta ce ta mutunta dokokin kasa da kasa, kuma tana yin iyakacin kokarinta na ganin an rage asarar fararen hula a Gaza. Ta ce ta kashe 'yan ta'adda fiye da 9,000 tare da zargin kungiyar Hamas da yin katsalandan a yankunan fararen hula, lamarin da ke da wuya a kaucewa hasarar fararen hula.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG