Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Mutum Da Ake Nema Kan Laifin Kashe Budurwarsa A Kenya Inda Ya Bar Gawarta A Filin Jirgin Saman Boston


Kevin Kangethe
Kevin Kangethe

An cafke wani mutum da ake nema kan laifin kashe budurwarsa tare da barin gawarta a wani wurin ajiye motoci a filin jirgin sama na Boston kafin ya tashi zuwa Kenya, kamar yadda ‘yan sandan Kenya suka bayyana a jiya Talata.

An kama Kevin Kangethe mai shekaru 40 a wani gidan rawa a ranar Litinin, biyo bayan wani rahoto da aka samu, kamar yadda Daraktan hukumar binciken manyan laifuka Mohammed Amin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Amin ya ce za a mika Kangethe zuwa ga hukumomin Amurka.

An gano gawar Margaret Mbitu mai shekaru 31 a farkon watan Nuwamba a cikin wata mota a garejin ajiye motoci na filin jirgin saman Boston Logan.

‘Yan uwan Mbitu sun sanar da bacewar ta kwanaki biyu kafin a gano gawarta.

A Boston lauyan gundumar Suffolk Kevin Hayden a Boston ya yaba da kokarin gano Kangethe.

"Ina matukar godiya ga jami'an tsaron difilomasiyya na ma'aikatar harkokin wajen Amurka, da FBI, da jami'an tsaron Kenya, da gwamnatin Kenya da kuma 'yan sandan jihar Massachusetts, saboda samun nasarar kama mutumin da ake zargi da yi kisan gilla ga Margaret Mbitu," in ji Hayden a cikin wata sanarwa.

David Procopio, mai magana da yawun 'yan sandan jihar Massachusetts, ya bayyana kamun a matsayin "wani kokarin hadin gwiwa da aka cimma a nahiyoyi."

Ofishin jakadancin Amurka ma ya yaba da kokarin jami'an tsaron Kenya na cafke wanda ya gudu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG