Kasar Burkina Faso na daga cikin yankin kudu da hamadar sahara da ke fama da tashe tashen hankula tun bayan yakin basasar Libya a shekara ta 2011.
Takunkuman, wanda ma'aikatar baitulmali da ma'aikatar harkokin wajen Amurka zasu fidda, na zaman takunkumai mafi zafi da aka sanya tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.
Firai Ministan Isra'ila ya fada a ranar Lahadi cewa, yuwuwar tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da mayakan Hamas zai jinkirta kai hari ta kasa ne kawai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda ya zama mafaka ga fiye da rabin al'ummar yankin da ke fuskantar rikici.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci babban bankin Najeriya CBN ya biya wani Bajamushe, Martin Gegenheimer Naira miliyan 63.7 da dala 10,000 bisa kama shi da tsare shi da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya NIS ta yi ba bisa ka'ida ba.
Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya shawarci 'yan Najeriya cewa, kada yi saurin yanke hukunci kan ayyukan shugaba Bola Tinubu danganed a halin da kasar ke ciki.
Babban hafsan tsaron Najeriya ya bayyana takaicinsa a yau Talata kan abin da ya kira rashin adalcin wasu kasashen da ke kin sayar da makaman soji wa Najeriya ta wajen rabewa da bukatar kare hakkin bil'adama.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce masu zanga-zangar suna zargin kasashen ne da goyon bayan Rwanda ta wajen amfani da 'yan tawayen M23.
Sanarwar Bankin na kunshe ne a cikin wani rahoto da aka fidda a makon jiya.
A jihar Kaduna kungiyoyin kare hakkin mutanen da Allah ya jarabce su da tawaya na ci gaba da ayyukan fadakarwa domin ganar da al’umma mahimman abubuwan da dokar kare hakkin masu bukata ta musamman ta yi tanadi a Najeriya.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Litinin cewa, rashin abinci mai gina jiki, da kuma yaduwar cututtuka na iya haifar da kazamin mutuwar yara a Gaza.
Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a ofishin ‘yan sanda a garin Zurmi da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, amma jami’ansu sun fatattaki su yayin da aka samu asarar rayuka a bangarorin biyu, in ji rundunar ‘yan sandan a ranar Litinin.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield, ta ce Amurka ba za ta goyi bayan kudurin ba a yadda aka tsara shi.
'Yan sandan Papua New Guinea sun ce mutane 53 ne aka kashe a wani rikicin kabilanci a yankin tsaunukan kasar da ke fama da rikice-rikice, wannan shi ne kisan kiyashi na baya-baya da aka gani mai alaka da dadaddiyar takaddama a yankin.
Domin Kari