Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Zargi Wasu Kasashe Da Rashin Adalci Na Kin Sayar Wa Najeriya Makamai


Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya ya bayyana takaicinsa a yau Talata kan abin da ya kira rashin adalcin wasu kasashen da ke kin sayar da makaman soji wa Najeriya ta wajen rabewa da bukatar kare hakkin bil'adama.

Kalaman na Janar Christopher Musa na kara jaddada daya daga cikin manyan kalubalen da kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka ke fuskanta wajen yaki da matsalar tsaro mai cike da sarkakiya.

"Duk da kudinmu, yana da wuya mu samu kayan aiki," a cewar Musa ga manema labarai a Abuja babban birnin Najeriya, inda ya tabbatar cewa akwai matukar bukatar kayayyaki kamar su jirage masu saukar ungulu, jirage marasa matuka da kuma motoci masu sulke.

Jami’an tsaron Najeriya sun kwashe shekaru da dama suna fuskantar zarge-zargen kashe-kashen ba bisa ka’ida ba da kuma kame ba bisa ka’ida ba. Akwai lokacin da Amurka da sauran manyan masu samar da makamai suka hana sayar da makamai saboda zarge-zargen.

A cikin watan Disamba, akalla fararen hula 85 ne suka mutu a lokacin da wani jirgin sojin Najeriya mara matuki ya kai hari kan jama’a lokacin wani taron addini a Kaduna na yankin arewa maso yammacin Najeriya, wanda shi ne na baya bayan nan cikin jerin irin wadannan lamuran.

Musa ya ce rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da inganta ayyukanta na kare hakkin dan adam kuma ta na hukunta jami’anta masu laifi. A yanzu haka ana gudanar da bincike kan zargin cin zarafi, kuma nan ba da jimawa ba za a fitar da rahoto kan harin na watan Disamba, in ji shi.

Sai dai kuma, babu wata shaida da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun samu ci gaba a fannin kare hakkin bil’adama, a cewar Isa Sanusi, darektan kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International a Najeriya.

Tallafin da sojojin Amurka ke bai wa Najeriya a wasu lokuta ya kan hada da horo kan yadda za a dakile hadurran da ke rutsawa da fararen hula, kamar yadda wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a watan Janairu kan hadin gwiwar tsaro.

Sanarwar ta ce a cikin watan Agusta ne Najeriya ta bayar da kudin farko na jiragen sama masu saukar ungulu guda 12 da kudinsu ya kai dala miliyan 997.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG