Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Raya Kasashen Afirka Ya Yi Gargadin Cewa Hauhawar Farashin Kayayyaki Na Iya Haifar Da Tarzoma A Tsakanin Al'umma


Bankin raya kasashen Afirka
Bankin raya kasashen Afirka

Sanarwar Bankin na kunshe ne a cikin wani rahoto da aka fidda a makon jiya.

Bankin raya kasashen Afirka ya yi gargadin cewa hauhawar farashin makamashi, abinci da sauran kayayyaki a wasu kasashen Afirka ciki harda Najeriya, na iya haifar da tarzoma a tsakanin al'umma.

Sanarwar Bankin na kunshe ne a cikin wani rahoto da aka fidda a makon jiya.

Bankin ya ce a hasashensa na shekarar 2024, karuwar farashin makamashi da abinci, tare da faduwar darajar kudin kasashen Angola, Habasha, Kenya da Najeriya, na iya haifar da rikicin cikin gida, duk da cewa nahiyar Afirka na nuna alamun samun ci gaban tattalin arziki.

An Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa
An Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

Bankin ya kuma ce tashin hankali a gabashin Turai da Gabas ta Tsakiya na iya haifar da kalubale wajen samar da kayayyaki, da kara hauhawar farashin kayayyaki a fadin duniya, lamarin da zai sa yanayin ya dada muni a Afirka.

Tuni aka fara zanga-zanga a wasu sassan Najeriya saboda yadda yunwa da tsadar rayuwa ke karuwa a Najeriya.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro Sanata Iroegbu ya yarda da hasashen Bankin na raya kasashen Afirka.

A cewarsa, “ko makaho ya san cewa ta yiwu a sami tarzoma a tsakanin al’umma saboda muhimman abubuwa 3 na rayuwa, abinci, matsuguni da tufafi, ma fi muhimmanci a cikinsu shi ne abinci, babu wanda zai iya rayuwa ba tare da abinci ba, kuma a yanzu hanyar da ‘yan Nijeriya suka dosa kenan."

A ranar Talata ne babban hafsan hafsoshin sojan Najeriya, Manjo Janar Christopher Musa, ya magana da manema labarai a Abuja kan halin da ake ciki inda ya ce; “Duniya baki daya na jin radadin, ba wai Najeriya ba ce kadai. An fuskanci ‘yar tarzoma nan da can, amma abin farin ciki shine, ita ma gwamnati ba ta barci, ta tashi tsaye wajen ganin an magance wadannan matsalolin. An kuma samar da matakan kawo sauki a duk fadin kasar."

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG