Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Yiwu Majalisar Dinkin Duniya Ta Kada Kuri'a Kan Tsagaita Wuta A Gaza Ranar Talata


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield, ta ce Amurka ba za ta goyi bayan kudurin ba a yadda aka tsara shi.

Akwai yiyuwar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai mambobi 15 zai kada kuri'a a ranar Talata kan bukatar kasar Algeria ta neman a tsagaita wuta a yakin Isra'ila da Hamas ba tare da bata lokaci ba, a cewar wani jami'in diflomasiyya, wani mataki da Amurka ta nuna alamar za ta hau kujerar na ki.

Makonni biyu da suka wuce ne kasar Algeria ta gabatar da daftarin kudurin farko. Amma Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce rubutun daftarin kudurin na iya kawo cikas ga " muhimmiyar tattaunawar" da ake yi da nufin yin sulhu a yakin.

A ranar Asabar ne Algeria ta bukaci kwamitin sulhun majalisar ya kada kuri'a a ranar Talata, in ji jami'an diflomasiyya. Don ya samu karbuwa, kudurin Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na bukatar akalla kuri'u tara dake goyon bayansa, kuma babu daya daga cikin kasashen Amurka, Birtaniyya, Faransa, China ko Rasha da zasu ki amincewa da shi.

"Amurka ba ta goyon bayan daukar mataki kan wannan daftarin kudiri. Idan har ya kai ga matakin kada kuri'a kamar yadda aka rubuta shi, ba za mu amince da shi ba," in ji Thomas-Greenfield a wata sanarwa a ranar Asabar.

Falisdinawa masu neman mafaka a Rafah
Falisdinawa masu neman mafaka a Rafah

Dama Amurka ta kan kare abokiyar huldarta Isra'ila daga matakin Majalisar Dinkin Duniya, kuma sau biyu ta na yin watsi da matakin majalisar tun daga ranar 7 ga Oktoba. Amma kuma sau biyu tana daga kafa, abin da ya ba majalisar damar aiwatar da wasu kudurori da nufin fadada ayyukan jin kai a Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta a fadan ba tare da bata lokaci ba don ayyukan jin kai.

A yanzu haka dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka, Masar, Isra'ila da Qatar don neman a dakatar da yakin a kuma sako mutanen da mayakan Hamas su ka yi garkuwa da su.

Yakin na Gaza ya fara ne a lokacin da mayakan kungiyar Hamas suka kai wa Isra'ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da mutane 253, bisa ga kididdigar Isra'ila. A wani mataki na ramuwar gayya, Isra'ila ta kaddamar da farmakin soji a Gaza wanda hukumomin lafiya suka ce ya yi sanadin kisan Falasdinawa sama da 28,000 yayin da ake fargabar wasu dubban gawarwaki sun makale a baraguzan gine-gine.

Kuri'ar da ta yiwu majalisar ta kada na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ke shirin kai hari a yankin Rafah da ke kudancin Gaza, inda Falasdinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka, lamarin da ya sa kasashen duniya suka nuna damuwa kan cewa irin wannan matakin zai kara tsananta matsalar jin kai a Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG