Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sandan Najeriya Sun Dakile Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Musu Da Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Jami’insu Daya


Wani bangaren ofishin ‘yan sanda da aka kaiwa hari
Wani bangaren ofishin ‘yan sanda da aka kaiwa hari

Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a ofishin ‘yan sanda a garin Zurmi da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, amma jami’ansu sun fatattaki su yayin da aka samu asarar rayuka a bangarorin biyu, in ji rundunar ‘yan sandan a ranar Litinin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce wasu da ake zargin ‘yan bindiga dauke da manyan muggan makamai ne suka kai wa ofishin ‘yan sandan hari da yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe wani babban jami’i tare da raunata wasu biyu.

“’Yan sandan da ke bakin aiki sun mayar da martani tare da dakile harin bayan wani mumunan harin bindiga da ya yi sanadiyar kashe ‘yan bindigar da dama, wasu sun kuma tsere da rauni daga harbin,” in ji Abubakar a wata sanarwa da ya fitar.

Jana'izar wasu da aka kashe
Jana'izar wasu da aka kashe

Abubakar ya ce ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike tare da tura karin ‘yan sanda domin su katange garin tare da kame ‘yan bindigar da suke gudu.

Mazauna yankin sun ce akalla mutane bakwai ne suka mutu a yayin harbe-harbe, ciki har da jami'in da ke kula da masu aikata laifuka na sashe.

Wani mazaunin garin Zurmi da ya shaida harin, Ibrahim Mohammed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho cewa an yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba tare da kona sashin ‘yan sanda.

Yan bindiga
Yan bindiga

Mohammed ya kara da cewa, "Sun yi kaca-kaca da wurin tare da kona wasu shaguna da motoci da ke kusa da ofishin 'yan sanda."

Wani mazaunin garin Usman Abubakar ya ce, "yanzu haka da nake magana da ku, sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen da ba a iya tantance adadinsu ba."

Gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai da ake kira ‘yan fashi da makami, sun yi barna a yankin arewa maso yammacin Najeriya a cikin shekaru uku da suka gabata, inda suka yi garkuwa da dubbai, da kashe daruruwan mutane, tare da hana tafiya ta hanya ko kuma yin noma a wasu yankunan.

Najeriya wadda ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka na fama da matsalolin tsaro da dama da suka hada da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa, lamarin da ya kai makura.

Matsalar rashin tsaro da ake fama da ita na kara ta’azzara matsalar tsadar rayuwa a wani bangare na sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi, wanda har yanzu bai yi cikakken bayani kan yadda yake shirin tunkarar lamarin ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG