Wasu masu zanga-zangar adawa da Rwanda sun kona tutocin kasashen yamma jiya Litinin a birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Wasu masu zanga-zangar da dama, sun lullube kansu da tutar DRC, suna tattake tutocin Amurka, na Tarayyar Turai, na Faransa da kuma na Poland.
Suna kuma ɗauke da kwalayen da aka rubuta: "Ku dakatar da kisan kiyashi a DRC," "Faransa = M23/Rwanda," da kuma "Duk wanda ya yi shiru shi ma da hannunsa."
Wani mai fafutuka ya shaida wa AFP cewa, "Kasar Rwanda na kashe mu a kowace rana, kuma kasashen duniya suna goyon bayanta, shi ya sa muka kona wadannan tutoci," in ji shi.
Masu zanga-zangar, wadanda galibinsu matasa ne, sun yi tattaki ne daga tsakiyar birnin zuwa hanyar zuwa Sake kafin suka koma. Majalisar birnin Goma dai ta haramta gudanar da zanga-zangar, amma an gudanar da zanga-zangar cikin lumana, ba tare da wata arangama tsakanin 'yan sanda da sojoji ba.
Dandalin Mu Tattauna