Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya Sun Yi Gargadin Cewa Mace-Macen Kananan Yara A Gaza Zai Kara Muni


Israel Palestinians Gaza Children
Israel Palestinians Gaza Children

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Litinin cewa, rashin abinci mai  gina jiki, da kuma yaduwar cututtuka na iya haifar da kazamin mutuwar yara a Gaza.

Makwanni 20 kenan da Isra'ila ta fara yaki da kungiyar Hamas a zirin Gaza, hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa , abinci da tsaftataccen ruwan sha sun yi karanci sosai a yankin Falasdinu, inda suka kara da cewa kusan dukkan kananan yara sun kamu da cututtuka masu yaduwa.

Akalla kashi 90 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Gaza suna fama da cututtuka guda ko fiye da haka, a cewar wani bincike na hadin gwiwa da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya kan yara, abinci da lafiya suka yi.

Kashi 70 cikin 100 sun kamu da gudawa a cikin makonni biyu kafin tantancewar, wanda ke nuna karuwar ninki 23 idan aka kwatanta da farkon shekarar 2022.

"Yunwa hade da cututtuka lamari ne mai kisa," in ji darektan kula da gaggawa na Hukumar Lafiya ta Duniya Mike Ryan a cikin wata sanarwa.

"Yaran da ke fama da yunwa, raunin rashin karfin jiki da yaran da suka razana, sun fi kamuwa da rashin lafiya, musamman masu fama da gudawa, jikin su ba zai iya shan sinadiran abinci masu gina jiki da kyau ba," in ji shi.

"Lamarin na da hadari da takaici, kuma ga shi yana faruwa a gaban idanunmu."

Harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,160 a Isra'ila, galibi fararen hula, a cewar wani alkaluman jami'an Isra'ila na AFP.

Hare-haren da Isra'ila ta kai kan Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 29,000 galibi mata da kananan yara, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas.

Tun da aka fara yakin, Gaza ta fada cikin matsalar karancin abinci mai gina jiki, tare da hanin shigowa da agajin daga waje yankin.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa sama da kashi 15 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekaru biyu a arewacin Gaza, daya cikin shida, na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun kara da cewa "Ko da yake an tattara bayanan ne a watan Janairu, mai yiyuwa lamarin zai fi haka kamari a yau."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG