Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Umurci CBN Ya Biya Wani Bajamushe Da NIS Ta Tsare Ba Bisa Ka'ida Ba Naira Miliyan 63.7


Kotun ECOWAS
Kotun ECOWAS

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci babban bankin Najeriya CBN ya biya wani Bajamushe, Martin Gegenheimer Naira miliyan 63.7 da dala 10,000 bisa kama shi da tsare shi da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya NIS ta yi ba bisa ka'ida ba.

A wani hukunci da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci babban bankin kasar CBN, da ya cire kudaden daga asusun gwamnatin tarayya da ke hannun ta, domin daidaita bashin da ya taso daga hukuncin 2021 da kotun alkalai ta kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yankewa Najeriya.

Mai shari’a Ekwo ya yi watsi da bayanin CBN cewa, a halin yanzu asusun gwamnatin tarayya na cikin gibi, wanda hakan ya sa ba za a iya biyan dukkan kudaden hukuncin ba.

Bajamushen, wanda ya ce ya ziyarci Najeriya ne a wata ziyarar aiki, ya bayyana cewa, yayin da yake komawa Kenya a ranar 23 ga watan Fabrairun 2020, jami’an hukumar kula da shige da fice ta Najeriya sun tare shi a kofar shiga jirgin saman Kenya Airways bayan an kammala dukkan ka’idojin tashin jirgi.

Ya ce jami’an NIS sun kama shi, suka kwace fasfo dinsa tare da tsare shi a wani dakin da ke da cunkuso daga 23 ga Fabrairu, 2020 zuwa 4 ga Maris, 2020, duk da cewa akwai ka’idojin cutar COVID-19 da ya kamata a kula.

A karshe dai ya kalubalanci kama shi da tsare shin da aka yi a gaban Kotun ECOWAS.

A cikin hukuncin ranar 4 ga Maris, 2021, wani kwamitin mutane uku na kotun , karkashin jagorancin shugaban kotun, Mai shari’a Edward Amoako Asante, ya bayyana kama Gegenheimer da tsare shi da aka yi a matsayin ba bisa ka’ida ba.

Kotun ta umurci gwamnatin Najeriya da ta biya shi N53,650,925 a matsayin diyya na musamman kan hasarar da ya samu da kuma kashe-kashen kudaden da ya yi a lokacin da hukumar NIS ke tsare da shi ba bisa ka’ida ba.

Kotun ta kuma umurci gwamnatin Najeriya da ta sake biyansa diyyar Naira miliyan 10 a matsayin diyya ga duk wani laifi da rashin adalci da aka yi masa na tauye masa hakkinsa, sannan kuma karin dala 10,000 da ya kashe yayin da yake neman beli.

Kotun ta ECOWAS dai ta umarci gwamnatin Najeriya da ta cire Bajamushen daga jerin sunayen da take sa ido, sannan ta gaggauta sakin fasfo dinsa na Jamus ba tare da wani sharadi ba, wanda jami’an gwamnatin Najeriya suka kwace ba bisa ka’ida ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG