Bayan mutuwar dan adawar Rasha Alexei Navalny da aka daure bisa dalilan kage, kuma kwana daya kafin cika shekaru biyu da Rasha ta fara mamayar kasar Ukraine, shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa zai sanya wa Rasha sabbin takunkumai sama da 500, lamarin da ke kara zafafa matsin lamba kan Vladimir Putin.
Gami da wadannan takunkuman, Amurka ta kuma sanya takunkumi kan fitar da kayayyaki zuwa wasu kamfanoni 100 "dake bayar da goyon baya ta bayan fage ga yakin Rasha. Muna daukar mataki don kara rage kudaden shigar Rasha ta fannin makamashi. Kuma na umurci tawagata da ta karfafa ba da goyon baya ga kungiyoyin farar hula, kafofin yada labarai masu zaman kansu, da masu fafutukar tabbatar da dimokradiyya a duniya,” in ji Shugaba Biden a wata rubutacciyar sanarwa.
"Shekaru goma da suka wuce, Putin ya mamaye Crimea, kuma ya kirkiro gwamnatocin jeka na yi ka a yankunan Luhansk da Donetsk na Ukraine. Shekaru biyu da suka wuce, ya yi ƙoƙarin ya shafe Ukraine daga doron duniya. Idan Putin bai dauki alhakin kashe shi ba da kuma barnar da ya haddasa, to zai ci gaba.
"Wadannan takunkuman za su shafi mutanen da ke da alaƙa da ɗaure Navalny a gidan kaso da sashen hada-hadar kuɗi na Rasha, da sashen bincike da sarrafa makaman soja, da masu kaucewa takunkumi a fadin duniya. Za su tabbatar da cewa Putin ya ga babban sakamako saboda kai farmaki a ketare da kuma danniya a cikin kasarsa.
" Takunkuman, wanda ma'aikatar baitulmali da ma'aikatar harkokin wajen Amurka zasu fidda, na zaman takunkumai mafi zafi da aka sanya tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.
"Tarihi na kallo," in ji Shugaba Biden. "Rashin tallafawa Ukraine a wannan muhimmin lokaci ba za a manta da shi ba. Yanzu ne lokacin da ya dace mu goya wa Ukraine baya kuma mu ci gaba da hada kai da kawayenmu da abokan huldarmu. Yanzu ne lokacin da za mu nuna cewa Amurka na goyon bayan 'yanci kuma ba ta amincewa da bukatun masu kama karya."
Dandalin Mu Tattauna