Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Super Falcons a Najeriya tana taka rawar gani a fafutukar da take yi don tunkarar gasar cin kwallon kafa ta duniya da za a gudanar a kasashen Australia da New Zealand kasa da kwanaki dari.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi da ke arewa ta gabashin Najeriya ta gargadi malaman addini da su kauce wa kalaman da za su iya harzuka magoya bayan mabiya darika daban-daban a jihar.
A ranar Laraba kungiyar real Madrid ta je har gidan Barcelona ta jefa kwallaye guda hudu bayan da Barcelonan ba ta sami damar jefa kwallo ko guda ba.
An sake zaban gwamnonin Bauchi da Gombe a wa’adi na biyu, biyo bayan zabubbukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da ya gudana a ranar asabar din data gabata.
Zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha da aka gudanar a jihohin Bauchi da Gombe ya samu halartar mutane maza da mata da suka cancanci kada kuri’a.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fidda sanarwar neman Honarabul Yakubu Shehu Abdullahi dan Majalisar wakilan tarayya ruwa a jallo a kan zarginsa da hannu wajen tada zaune tsaye, lamarin da ya janyo kisan kai a garin Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.
A ci gaba da kidayar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 daga kananan hukumomin jihar Bauchi, zuwa yanzu Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne ke kan gaba da rinjaye kan sauran abokan hamayyarsa.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya umarci al’ummomin jihar da su kashe masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’addan da suke yankunansu. Gwamnan yayi wannan ikrari ne a garin Rimi dake yankin karamar hukumar Alkaleri.
A wata babbar nasara da 'yan sanda su ka samu a jihar, sun aika da wasu mutane 12 da ake zargin 'yan bindiga ne zuwa lahira
Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe mutane 11 a wasu kauyukan karamar hukumar Alkaleri, dake jihar Bauchi. Tare da kona gidaje masu gidajen al’umma da yin awon gaba da kayan abinci da dabbobi.
A wani yinkuri na neman samun romon dimokaradiyya, wasu talakawan jihar Bauchi ta arewacin Najeriya, sun yi barazanar kaurace ma kada kuri'a muddun ba a gyara masu hanyoyi kamar yadda aka sha yin masu alkawari ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta cafke wata mata mai suna Maryam Ibrahim ‘yar shekara 20 bisa zargin ta kashe kishiyarta mai suna Hafsat Ibrahim ta hanyar kwada mata tabarya a kai.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da aikin hakar arzikin man fetur na farko a Arewacin Najeriya.
Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar PDP G-5 ta kai ziyara wa Gwamnan Jihar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed, a matakin nemo hanyar sulhunta rikicin dake neman kawo baraka a tsakanin gwamnonin da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyar.
Ma’aikatar Shari’a ta jihar Bauchi ta bijiro da wannan tsari ne ta hanyar kafa kananan kotunan domin karbar kudaden daga hannun mutanen da ake bin su bashi
Akwai dalilai masu yawa da za su nuna wajibcin tanadi don gaba, ciki har da na ritaya, ilimi, siyan dukiya, aure, da dai sauransu.
Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya duba irin hobbasar da gwamnatocin jihohi ke yi wajen habbaka harkokin kasuwanci da zasu bada dama wajen kafa kamfanoni don bunkasa tattalin arzikin jihohin da ma kasa baki daya.
A cigaba da wasan kwallon kafa na mata na Duniya a Indiya, 'yan kasa da shekaru 17,matan Najeriya , da ake cema Flamengoes, Kasar Colombia ta fitar da kungiyar kwallon kafar Najeriya Flamengoes
Jiga-jigan ‘ya’yan babbar jam’iyar adawa ta PDP daga sassan Najeriya karkashin jagorancin shugaban jam’iyar ta kasa, Dr. Iyorchia Ayu, sun kai ziyarar marabtar wasu ‘yan siyasa sama dubu 140 da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar ta PDP.
Domin Kari