Wannan nasara da Madrid ta samu a kan Barcelona ita ta bata damar buga wasan karshe ta cin kofin Copa del Rey.
A gasar Premier ta kasar Ingila kuma kungiyar Manchester United ta sami nasara a kan Brantford da ci daya mai ban haushi. Wannan nasarar da Manchester ta samu ta bata damar dagawa zuwa ta hudu a teburin gasar.
Dan kwallon kafa da ke buga wa klub din Paris Saint-German wasa, Kylian Mbappe, yana karbar har kashi goma na yawan albashinsa na wata-wata a matsayin kudin bonos na shekara daga klub din.
Mbappe mai shekaru 24, yana samun Euro million 60 a kowacce shekara a matsayin bonos saboda yi wa klub din ladabi, a yayin da ya ke karbar Euro miliyan 6 a kowane wata a matsayin albashi, a cewar kafar l’equipe.
Kyalian Mbappe na daya daga cikin masu kudi a fannin kwallon kafa, ya nuna biyayya ga klub din, a yayin da aka yi ta kai komo sabili da kin amincewa ya koma klub din real Madrid a kakar wasan kwallon bara.
Wani dan wasan kwallon kafa ya kirkiri jin ciwo na da gan-gan domin ya ba abokin wasansa dama ya yi bude baki sabili da azumin da ya ya ke yi, wannan abu ya faru ne a ranar Asabar a filin da ake buga wasa tsakanin klub din Fiorentina da Milan, inda aka ga dan wasa Luka Ranieri ya kirkiri jin ciwo na karya domin ya ba Sofyan Amrabat damar shan ruwa bayan azumi.
A gefe guda kuma dan damben zamani Anthony Joshua, dan Najeriya mazaunin Ingila, ya ce Laura Woods, wata mace mai gabatar da shirye-shiryen harkokin wasanni, ita ce macen da yake mafarkin mallaka. Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da suka yi da ita biyo bayan nasarar da ya samu a kan wani dan damben boxing dan kasar Ingila mai suna Jermaine Franklin a ranar Asabar.
Nasarar da Anthony Joshua ya samu ita ce ta farko tun bayan lokacin da ya sha bugu a hannun Oleksandr Usyk dan kasar Ukraine a shekarar 2020.
Shi ko Oscar Pistorius mai shekara 36, dan wasan nan na motsa jiki a bangaren masu bukata ta musamman dan kasar Afrika ta Kudu, wanda aka daure shi har tsawon shekaru 13 saboda kashe budurwarsa mai suna Reeva Steenkamp a shekarar 2013, a halin da ake ciki ya nemi mahukuntan kasar su bashi beli. Sai dai kuma a nata bangaren a zaman da ta yi don nazartar wannan bukata, hukumar kula da sha’anin beli ta kasar ta ki amincewa, inda ta ce yana da sauran shekara daya da rabi da zai kara a gidan yari kafin a duba cancantar bashi beli.
Saurari rahoton Abdulwahab Muhammed: