Wasu daliban gaba da makarantun firamare a jihar Bauchi sun yi tattaki a kan titunan birnin Bauchi a farkon makon nan don bayyana damuwarsu game da sabon salon tsarin da gwamnatin jihar ta bijiro da shi na ware makarantun maza zalla da mata zalla.
Shirin ya duba jerin sunayen kasashen da suka yi fice a fagen taka leda da kuma sunayen kasashen Afrika da matsayinsu a fagen buga kwallo a duniya. Bayan haka, shirin ya duba batun ce-ce-ku-cen da ke faruwa a fagen siyasar neman shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya
A cigaba da tabarbarewar tsaro a Najeriya, tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu Dogara, ya yi zargin an yi shirin kashe shi. 'Yan sanda dai sun ce sun damke wani da ya amsa laifin, kuma su na cigaba da bincike.
Matasa wajen talatin daga Jihohin Arewa Maso Gabas, hukumar Bunkasa Shiyyar Arewa Maso Gabas ta koya masu dogaro da kai, ta hanyar koya musu sana’ar kere keren na’urorin da ba su kawo lahani ga yanayi, da suka hada da risho da sarrafaffen datti domin yin Makamashi.
Hukumar dake kula da Kafofin yada labarai na Radiyo da Telabijin na Kasar Amurka a Najeriya ta gudanar da taron bita wa ‘yan jarida masu bada rahoto game da harkokin kiwon lafiya, a jihar Bauchi.
Yau za mu fi karkata ne ga gwabzawar da ake kan yi a Ingila a Wasannin Kasashe Rainon Ingila (CGames)
Gwamnan jihar Bauchi ya gargadi masu sarautun gargajiya da jami'an tsaron da ake hada baki da su wajen baiwa yan bindiga masu tayar da kayar baya mafaka ko bayanai.
Jakadan Kasar Sin a Najeriya ya kammala ziyarar aiki na kwanai biyu a Jihar Bauchi, inda ya gana da Jami’an gwamnati da kungiyoyin ‘yan kasuwa da masana’antu, da su ka tattuna akan wasu yarjejeniyoyi na hadin gwiwa , tsakanin kasar Sin da Najeriya.
Yau fagen labaran wasannin, a maimakon labarin shahara a fafatawar da ake yi kawai, zai fi mai da hankali ne kan shahara wajen mallakar dukiyar da ake samu wajen daya daga cikin wasannin, wato Golf.
Har yanzu Pele ya fi kowane dan wasan Brazil yin fice. Wannan ko ya tabbata a wani jerin sunayen gwarazan 'yan wasan Brazil
Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, matashin da aka kwakulewa idanun ya nemi da a bi masa kadınsa.
An kaddamar da Hukumar da zata rika daukar dawainiyar jinyar marasa galihu dake cikin al’umma a duk fadin jihar Bauchi.
Tsohon shugaban hukumar ta NFF, Alhaji Aminu Maigari, wanda shi ma ya jagoranci hukumar a baya-bayan nan, ya tabbatar da sako Toro.
Bincike ya nuna cewa iyalan tsohon sakatare janar na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya Alhaji Sani Ahmed Toro, wato Yeriman Toro, sun fara magana da mutanen da suka sace shi tare da wasu mutane biyu akan hanyarsu ta zuwa Bauchi daga Abuja.
An fara jigilar Alhazan ne daga filin jirgin saman sauka da tashi na kasa da kasa dake Bauchi, inda ake sa ran alhazan jihohin Bauchi , Gombe da kuma na jihar Filato za su tashi daga filin jirgin na Sir Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.
Ya zuwa yanzu an tantance kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya da kasar za ta karbi bakunci a watan Nuwamban bana.
Hukumar zabe ta INEC a jihar Bauchi ta bukaci ‘yan siyasa da kuma al’ummar jihar da su hanzarta karban katunan zabensu da aka yi wa rajista.
Rahotanni daga jihar Bauchi, na nuni da cewa za a sake zaben ne bayan da dan takarar da aka zaba ya janye.
Bincike ya nuna cewa, rikicin da ya faru a Unguwar Yelwa, da ke Karamar Hukumar Bauchi, Jihar Bauchi, ba ya da nasaba da addini ko kuma kabilanci.
Zaben fidda gwani na gwamnoni a Jam’iyar PDP a Jihohin Bauchi da kuma Gombe ya samar da sabbin fuskoki a fagen siyasa.
Domin Kari