Bikin ranar yin ajiya a bankuna, rana ce ta duniya da aka ware don nuna muhimmanci da kuma wajibcin tanadi a bankuna don gaba.
Daga cikin dalilan da suka nuna wajibcin yin tanadi don gaba, akwai na ritaya, ilimi, sayen dukiya, aure, da dai sauransu.
A jihar Bauchi, mai kula da shiyya na hukumar Inshoran tanadi, Alhaji Ajiya Bazarma ya gudanar da taron fadakarwa ne wa daliban makarantar sakandare da nufin cusa musu dabi’ar yin ajiyan kudade tun suna yara kanana.
“Wannan taron fadakarwar ba Najeriya kadai bane duk duniya ne ake yi, rana ce da aka ajiye saboda a rika fadakar da mutane musamman yara akan yadda za su yi adana su tashi da hali na adana….” Alhaji Ajiya Bazarma ya ce.
“Gaskiya na karu sosai, abin da ya sa na fadi haka, duk lokacin da muka samu kudinmu, mu kai shi banki mu ajiye, duk wata damuwar da ta so mana za’a iya cirewa a yi anfani da shi.” In ji Kamal Idris, daya daga cikin dlaiban Government Comprehensive School Bakari Dukku da aka fadakar.
Domin jin cikakken bayani, saurari rahoto cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad.