Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi Aminu Alhassan ya yi wannan gargadi a karshen zaman da kwamitin tsaro ya yi don nazartar matsalolin tsaro da ke kokarin kunno kai a jihar ta Bauchi.
Idan za’a iya tunawa dai a cikin makon da ya gabata ne, wani malamin addini Musulunci a garin Bauchi mai suna Dakta Idris Abdu’aziz Dutsen Tanshi, a cikin hudubar da ya gabatar, ya yi bayani kan fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W), da kuma wasu mashahuran malaman addinin Musulunci da suka gabata da wasu ke ganin tozarci ne ga wadannan bayin Allah.
Kalaman ya janyo martani daga ciki da kuma wajen jihar Bauchi, a yayin da aka samu wasu malaman addinin musulunci suka zo Bauchi domin tabbatar da abubuwan da suke ji da kuma gani a kafofin sada zumunta.
Hakan ne ya sa kwamitin tsaro na jihar Bauchi ya gudanar da zama domin tabbatar da cewa zaman lafiyan da ke jihar Bauchi bai samu cikas ba.
Da yake jawabi ga wani taron manema labarai a Bauchi, Kwamishin yan sanda, Alhassan Aminu, “ya ce sun zauna ne a kan abun da ya kamata jihar ta ci gaba a kai, a hakikanin gaskiya akwai abubuwa guda biyu da suke tasowa manya guda biyu wanda 'yan kananan yara suke tasowa da nufin sara suka, abun yana bata musu rai kuma yanzu dole ne su dauki mataki a kai.”
Aminu ya ce haka kuma game da maganar addini sun yi magana sosai a kai, sun fahimci cewa jihar Bauchi Allah ya yi mata darajar samu addinai da yawa kuma a cikin kowane addini akwai bangare- bangare, bai kyautu yadda wani yake yin na shi ya zama yana shafar na wani ba duk kowa yana da iko da ya yi addinin shi yadda yake so.
Ya kara cewa sun yi maganganu da yawa sun tattauna sannan kuma akwai abubuwa da suka fito da su, in sha Allahu za su zo kan wannan gabar yadda kowane mutum zai san da cewa yana da mutunci shi yana darajar shi don addinin shi bai kyautu wani ya soki addinin shi ba.
Da yake tsokaci kan kalaman malamin, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a a jihar Bauchi, Barista Garba Hassan, ya ce wannan magana ce wacce babu wani tashi hankali a ciki, magana ce wacce aka bata wata fassara daban, kuma kowane Musulmi ya san ga matsayi Allah (S.W.A) kuma ga matsayi na Annabi (S.A.W).
Ya ce babu wata magana wanda zai zo ya zamanto ya daga hankali a ce Annabi (S.A.W) shi ne wanda yake dan gatan Allah babu wanda Allah yake so a cikin halitta kamar Annabi Muhammadu (S.A.W.), saboda haka Allah ake roko ya biya bukata, Annabi kuma shi ake so.
Ya kara cewa kuma kana da damar ka roki Allah (S.W.A), Ya Allah don so da kake yi wa Annabi (S.A.W) kayi min abu kaza, idan ka fadi haka misali ka ba da matsayi ga Annabi da babu wanda ya fi shi daraja.
A nasa bangaren, Malami a Makarantar Nazarin Shari’ar Musulunci da ke Misau, Dakta Ibrahim Imam, ya ce hakika wannan neman tashi hankali ne da hana kasa zaman lafiya kuma ya yi kira da gwamnati da ta hada kan al’ummarta a zauna lafiya, kuma abun da zai kawo hakan shi ne a hana wani zagin wasu.
Saurari cikakken rahton Abdulwahab Muhammad: