Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Honarabul Yakubu Dogara Ya Maida Martani Kan Cigiyar Honarabul Yakubu Shehu Abdullahi Da ‘Yan Sanda Ke Yi


Tsohon kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara
Tsohon kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fidda sanarwar neman Honarabul Yakubu Shehu Abdullahi dan Majalisar wakilan tarayya ruwa a jallo a kan zarginsa da hannu wajen tada zaune tsaye, lamarin da ya janyo kisan kai a garin Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.

Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya Honarabul Yakubu Dogara, ya ce ‘yan sandan ba su bi ka’ida ba kan yadda suke neman Honarabul Yakubu Shehu Abdullahi, dan majalisar tarayya da ke wakiltar mazabar cikin garin Bauchi, a saboda haka za su kalubalanci hukuncin a kotu.

A wani taron manema labarai da Mr. Yakubu Dogara ya kira, ya zargi hukumar ‘yan sanda da keta hakkin dan majalisar, domin ya ce akwai ka’idoji da ake bi idan ana neman dan majalisa ya gabatar da kansa gaban hukumar ‘yan sanda.

Dogara Yakubu.
Dogara Yakubu.

Iyalan Honarabul Yakubu Shehu Abdullahi, da hukumar ‘yan sanda ke nema, sun bayyana cewa lamarin ya basu mamaki ya kuma tada musu hankali sosai.

A nata bangaren hukumar ‘yan sanda a ta bakin kwamishinanta Aminu Alhassan, yace ana neman dan majalisar ne a matsayinsa na Yakubu Shehu Abdullahi kuma an bi dukkan ka’idoji da dokar kasa ta Shimfida.

'yan sanda na zargin dan majalisar ne bayan da ta fara bincike kan wani rikici da ya barke a garin Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu 15.

XS
SM
MD
LG