Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Kananan Hukumomi 11 Na Jihar Bauchi Sun Gabatar Da Sakamakon Zabensu


‘Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kada kuri’a a Gundumar Ajiya dake karamar hukamar Yola, Jihar Adamawa
‘Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kada kuri’a a Gundumar Ajiya dake karamar hukamar Yola, Jihar Adamawa

A ci gaba da kidayar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 daga kananan hukumomin jihar Bauchi, zuwa yanzu Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne ke kan gaba da rinjaye kan sauran abokan hamayyarsa.

Sakamakon da aka bayyana kai tsaye daga cibiyar tattara sakamakon da ke shalkwatar INEC a Bauchi, ya yi nuni da cewa a karamar hukumar Warji APC ta samu kuri'u 11,862, PDP 17,732, NNPP 424 sai kuma LP mai kuri'u 185.

A karamar hukumar Bogoro, APC ta samu kurI'u 4,850, LP 6,866, NNPP 798, sai kuma PDP 15,156.

Sakamakon ya kuma nuna cewa a karamar hukumar Dass APC ta samu kuri'u 10,939, LP 705, NNPP 397, sai kuma PDP ta samu kuri'u 13,242.

A karamar hukumar Jama'are, APC ta samu kuri'u 8,410, LP 22, NNPP 3,638, PDP 12,535. A Dambam, APC ta samu kuri'u 7,588, LP 42, NNPP 2,586, PDP kuma 12,203.

Hakazalika, a karamar hukumar Giade PDP ce ke kan gaba da kuri'u 11,977, APC 10,382, NNPP 4002, LP 17. Sai kuma a karamar hukumar Darazo inda APC ta samu kuri'u 16,070, PDP 17,459, NNPP 1,895.

A karamar hukumar Kirfi, APC ta na da kuri'u 9599, PDP 13,231, NNPP 1,544, LP kuma 33, yayin da a karamar hukumar Misau APC ta samu 14,199, PDP 18,354, NNPP 4,115, jam'iyar Zenith Labour 24, PRP kuma 77.

A karamar hukumar Katagum APC ta samu kuri'u 20,030, PDP 22,987, NNPP 9,672, LP 493, Zenith Labour 27, PRP kuma kuri'u 22.

Karamar hukumar Ganjuwa kuma APC ta samu kuri'u 13,021, PDP 17,380, NNPP 4,287, LP 222, Zenith Labour 21, PRP kuma ta samu kuri'u 32.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG