Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11 a Yankin Akaleri Ta Jihar Bauchi


BAUCHI: Sojojin dake Bauchi sun kashe wasu bata gari, masu satar mutane da fashi da makami
BAUCHI: Sojojin dake Bauchi sun kashe wasu bata gari, masu satar mutane da fashi da makami

Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe mutane 11 a wasu kauyukan karamar hukumar Alkaleri, dake jihar Bauchi. Tare da kona gidaje masu gidajen al’umma da yin awon gaba da kayan abinci da dabbobi.

Masu tayar da kayar baya sun addabi yankunan da kai hare-hare wanda ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi, tare da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.

Da yake tabbatarwa wakilin sashen Hausa faruwar lamarin mazaunin yankin, Alhaji Abdu, ya ce masu garkuwa da mutane ne suka afkawa kauyukan da harbe-harbe, wanda lamari da ya zama ruwan dare a yankin.

Kafin wannan hari da yan bangar dake kare al’umommin yankunan sun shiga daji suka sami nasarar ceto wata mata da ‘yarta a hannunsu, tare da kwato wata bindiga mai harbi har 48 daga maboyarsu.

Mazauna yankunan karamar hukumar Alkari na kallon rashin zaman lafiya dake addabarsu na da alaka da ma’adanan arzikin Man fetur da aka gano a jihar Bauchi, hakan yasa suke kira ga gwamnatin tarayya da kai musu agaji.

Hon Yusuf Mohammed, dan Majaslisar Dokokin jihar Bauchi, dake wakiltar Alkaleri, ya tabbatar da kisan mutane 11 a garin Rimi tare da sace dabbobi da kona kashi biyu cikin uku na garin.

Sai dai a bangaren hukumar yan sandan jihar Bauchi, a wata sanarwa da ta fitar ta hannun kakakinta SP Ahmed Wakil, ta ce ta tura jami’anta don fatattakar yan bindigar.

Don Karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG