Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Super Falcons Ta Lallasa Kasar New Zealand Da Ci Uku Ba Ko Daya


Super Falcons
Super Falcons

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Super Falcons a Najeriya tana taka rawar gani a fafutukar da take yi don tunkarar gasar cin kwallon kafa ta duniya da za a gudanar a kasashen Australia da New Zealand kasa da kwanaki dari.

Wani abun farin ciki shi ne kungiyar kwallon kafar ta Super Falcons ta lallasa kasar New Zealand, daya daga cikin kasashe biyu da suka dauki dawainiyar gudanar da gasar cin kofin da ci 3 ba ko daya a gasar sada zumunci da aka yi ranar Talata a birnin Antalya da ke Australia.

Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar Super Falcons ke samun nasara a gasar sada zumunta ta kasa-da-kasa, inda ta ci kasar Haiti 2 da 1.

Wani dan dambe boxing na gwamutse, wato bayan duka da hannu ana yi da kafa, mai ruwa biyu dan kasar New Zealand da kuma Najeriya, mai suna Israel Adesanya, yace Najeriya ta baci da harkar cin hanci da rashawa. Ya kara da cewa yana kaunar Najeriya, amma tana da kalubale da yawa.

Adesanya yace shugabanni a Najeriya suna rige-rigen wawure kudaden al’umma. Ya kuma ce yana son ‘yan Najeriya amma abin takaici shi ne, gwamnati da sauran mutane na ta kokarin samun hanyoyin sace dukiyar kasa.

Adesanya shi ne ya wakilci Najeriya a wasan da aka gwabza tsakaninsa da Alex Pereira dan kasar Barazil a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekarar ta 2023, inda ya samu kudi dala miliyan uku da dubu goma sha takwas.

Wata mace 'yar kwalisa mai shekaru hamsin ‘yar kasar Spaniyya mai suna Sonia Monroy, tace dan kwallon duniya Cristiano Ronaldo, ya sace mata baccin dare kafin su hadu da macen da suke tare a yanzu wato Geogina Rodriguez.

Ita dai Sonia Monroy 'yar film ce, kuma mawakiya mai gabatar da shirye-shirye a kafar yada labaran fox a fannin wasanni. Akwai mutane sama da dubu dari shida da sittin da bakwai da ke bibiyarta a shafin Instagram.

Ana zargin Sadio Mani da naushin fuskar Leroy Sane, wani abokin wasansa da suke klub din Bayern Munich a ranar da Manchester City ta lashe klub din Bayern Munich da ci 3 ba ko daya a fafatawar da suka yi a daren Laraba a Ingila a zagayen farko na ci gaba da gasar cin kofin zakarun kasashen Turai zagayen kwata final

An bada rahoton cewa Sadio Mane ya naushi Leroy Sane a baki a lokacin da suke mahawara a dakin canjin kayan ‘yan wasa. Abu na gaba shi ne Mane zai iya fuskantar ladabtarwa daga klub dinsa sabili da abin da ya aikata.

A halin da ake ciki, klub din Paris Sait Germain ko kuma PSG a takaice, yana neman wanda zai maye gurbin Sergio Ramos mai tsaron gida. An dai ruwaito cewa klub din PSG na zawarcin wani matashi mai suna Rafa Marin da ke klub din Real Madrid a fafutukar samo mai tsaron gida na tsawon lokacin da zai maye gurbin Sergio Ramos.

Matashin mai shekaru 20 yana wasa ne a sashen Academy na klub din Real Madrid, a yayin da shi kuma Sergio Ramos, yake cikin watannin karshen kwantiraginsa da klub din PSG, kuma alamu na nuni da cewa baza a sabunta kwantaragin nasa ba.

Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG