Kotun dai ta zauna ne cikin tsauraran matakan tsaro bisa jagorancin alkalin aro mai suna Justice Evelyn Anyadike sanadiyar lallurar da alkalin na asali Justice Fati Liman ke fama da ita.
Hukumar EFCC dai ta gabatar da caji dai dai har guda ashirin da takwas ta take tuhumar Sule Lamido da 'ya'yansa Aminu da Mustapha da kuma wani Aminu Wada Abubakar.
Hukumar ta EFCC tace tana zargin tsohon gwamnan ne da laifin cewa kamfanonin da yake da hannun jari a cikinsu sun yi mu'amalar kwangila da gwamnatin jihar Jigawa a lokuta daba daban cikin shekaru takwas da yayi yana mulkin jihar. A cewar EFCC yin hakan ya sabawa dokar kasa.
Jimlar kimanin nera biliyan guda da miliyan dari uku ne hukumar ke tuhuma an yi mu'amalar kwangila tsakanin gwamnatin jihar Jigawa da kamfanonin. To saidai Sule Lamido da 'ya'yansa da Aminu Wada Abubakar sun musanta zargin.
Lauyansu ya bukaci kotun ta bada belinsu tunda zargi ne kawai. Amma lauyan EFCC ya nemi kotun ta yi watsi da bukatar yana cewa da misalin karfe biyar na yammacin jiya Laraba suka samu takardar neman belinsu maimakon sa'o'i 24 da doka ta tanada.
Alkalin ta bukaci lauyan su wadanda ake zargin ya sake mika takardar neman belinsu ga alkalin wucingadi da ake sa ran zai gudanar da aiki a cikin hutu tunda daga gobe Juma'a alakalan kotunan Najeriya zasu je hutun shekara shekara na watanni biyu.
Amma yanzu Justice Anyadike ta bada umurnin a kai wadanda ake tuhumar gidan wakafi har sai sun samu beli ko kuma an cigaba da karar ranar 28 ga watan Satumba.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5