Alhaji Bashir Dalhatu yace ya fadawa shugaban kasa cewa ya ziyarci jihar kaman sau hudu ke nan tunda ya kama mulki abun da ya nuna cewa yana kaunar jihar.
Duk lokancin da ya zo jihar yana yi masu alkawura kuma yana cikasu. Ya yiwa jihar ayyuka. Misali ya gina makarantu da jami'a da tituna da bunkasa ayyukan harkokin noma da kuma sabon filin saukar jiragen sama da ma wasu abubuwa da yawa dake kara inganta jihar.
Su dattawa sun yiwa shugaban kasa godiya da kuma nuna masa suna nan. Kamar yadda yake yi masu abubuwan alheri su ma zasu yi mashi abubuwan alheri. Dama sun saba taimaka masa. Idan kuma ya zo ya sake tsayawa zasu taimaka masa kamar yadda ya cancanta.
Dangane da cewa dangantaka ta gurbace tsakanin shugaban da gwamnan jihar Alhaji Bashir Dalhatu yace ya fadawa shugaban cewa kodayake suna goyon bayan gwamnati da shi amma goyon bayan ba makaho ba ne. Goyon baya ne idan suka ga wani abu zai goce ko ya gurbace to gwamnansu yana da wannan hali ya jawo hankali domin a gyara. Yana hakan ne ba wai domin baya so ba ko baya kauna amma domin a dada daidaitawa a yi tafiya sosai kuma mutanensu su ji dadin tsarin da kuma tafiyar gwamna da shugaban kasa.
Alhaji Bashir yace shugaban kasa yace ya gode da abubuwan da suka fada. Godiyar da suka yi zata kara masa kaimin kawo abubuwan jin dadi da na cigaban kasar. Shugaban kasa yace zai cigaba da yin shawara da gwamnan jihar Sule Lamido kafin ya sake komowa ya kawu wasu abubuwa domin ya zama kaman dan gida a jihar.
Shugaban kasar yace a Najeriya ana ganin kamar akwai gurbacewar danganta dashi da gwamna Sule Lamido amma ya tabbatar cewa gwamnan ya taimaka masa a shekarar dubu biyu da bakwai. Shugaban yace gwamna Lamido ba mutum ba ne dake magana da bangarori biyu na bakinsa. Abun da yake ransa shi yake fada ba wai domin yana kinsa ba ko baya goyon bayansa ba amma domin a daidaita kuma gaskiyarsa daya ce.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.