Tawagar dattawan jam’iyyar PDP da ta ziyarci gwamna Sule Lamido na jihar Jigawa ta ce ya na nan cikin jam’iyyar daram; so kawai ya ke a rinka bin ainihin ka’idar jam’iyyar. A hirarsu da Aliyu Mustaphan Sakkwato, daya daga cikin dattawan jam’iyyar, Sanata Walid Jibrin, wanda ya ce ba a matsayin kwamitin amintattun jam’iyyar su ka ziyarci gwamna Lamidon ba, ya ce sun kai ziyara jihar jigawa wurin gwamnan ne karkashin wani shiri na musamman na sasanta ‘yan jam’iyyar. Ya ce akwai irin wannan kwamiti din har guda shida.
Da Aliyu Mustapha ya tambaye shi ko sun iya shawo kan gwamna Sule Lamido ganin bai fito fili ya bayyana goyon bayansa ga batun tsai da Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar PDP tilo a zaben Shugaban kasa na 2015 ba, Sanata Jibrin bai yi wani takamaiman bayani ba, illa kawai cewa su shawara su ka je yi. Ya ce Sule Lamido ya ce a bi ka’ida kawai.
Da Aliyu Mustaphan ya tambayi Sanata Jibrin ko shin sun matsa ma gwamna Lamido ya janye takararsa ta Shugaban kasa, sai Sanata Jibrin ya ce ai gwamna Sule Lamido bai ma bayyana masu cewa ya na sha’awar takarar Shugaban kasa ba.