A 'yan makonnin da suka gabata sakataren jam'iyyar PDP reshen jihar Jigawa Aminu Jahun yace suna muradun Sule Lamido ya nemi tsayawa takara a karkashin lemar PDP. Haka ma abun yake ga mutane irin su Sale Taki, wani na hannun daman gwamnan kuma tsohon shugaban karamar hukumar Kazaure.
Sale Taki yace a duk cikin 'yan siyasan arewa babu wanda yayi NEPU, PRP, SDP, G7 wadanda suka yi karo da sojoji domin dimokradiya ta tabbata. Duk cikinsu shi kadai aka daure domin ya tsaya tsayin daka sai an yi dimokradiya. Cikin shekara bakwai Sule Lamido ya juye jihar Jigawa inji Sale Taki. Yace yadda Sule Lamido ya canza Jigawa haka zai canza Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
To sai dai batun kiran Sule Lamido ya tsaya neman shugabancin Najeriya tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ne ya fara. Shi ya fito karara ya ce babu wanda ya dace ya zama shugabanNajeriya irin Sule Lamido. Ya fada ba sau daya ba ba sau biyu ba. Bara ma cewa yayi PDP ta tsayar da Sule Lamido a matsayin shugaba Rotimi Amechi kuma, wato gwamnan Rivers a matsayin mataimakinsa. Ranar Litinin ma da ta bagata tsohon shugaban ya sake sabunta batun yayin da ya kai wata ziyara Dutse babban birnin jihar Jigawa inda yace Lamido ya mallaki duk abun da ake so ga shugaba.
Tuni maso tsokaci a harkokin siyasa suka soma yin tsokaci akan batun Sule Lamido. Malam Albati Bako daraktan cibiyar harkokin dimokradiya ta kasa da kasa yace Obasanjo yayi magana a dunkule. Wato yana gayawa PDP ga wata mafita wadda zata rudawa APC lissafi.
Ga rahoton Mahmud Kwari.