Ya ce ana batun gyare-gyaren jam'iyya bisa ga tafarkin tsarin jam'iyya da kundun tsarin mulkin kasa. Ya ce duk wani abu na harsashen cigaban kasa duk an karya su. Ya ce lamarin ya baci har wasu 'yan jam'iyyar da suka kai matsayin gwamnoni sun fice sun tafi. Ya ce an riga an yi muguwar barna. Abun da ya fuskanci PDP yanzu shi ne yaya za'a yi gyara har a samu yaddar jama'a su amince za'a yi gyara domin a cigaba.Ya ce ta kowane fanni an yiwa jam'iyyar barna.
Dangane da ko saukar Bamanga Tukur tamkar kuwa bayan hari ce watakila ma ba zata yi anfani ba domin ba'a yita lokacin da kuka bukaci a yi ba. Ya ce makomar dimokradiya a Najeriya ake magana kai. Ya ce idan ana ganin wannan abun da ya faru a PDP annobar PDP ce kawai to annobar ta riga ta yadu ta shiga gidan kowa har da ita APC inda a ke dora 'yan PDP bisa wadanda suka kafa jam'iyyar. Wannan ma kama karya ne. Ya ce ginin kasa baya yiwuwa idan babu doka muddin aka cigaba da mulkin kama karya ko a jam'yya ko a gwamnati.Mulkin kama karya Bamanga Tukur ya yi a PDP bayan jam'iyyar ta kwashe shekaru takwas tana shugabancin kasar.
Tambaya ita ce menene makomar dimokradiya a Najeriya. Lamido ya ce sharudan da a ke fada ana maganar gyara ne. Misali an dakatar da gwamna a Sokoto an yi a Adamawa har da Rivers da korar Baraje. Kokarin da za'a yi yanzu shi ne yadda za'a rayar da dimokradiya tun daga kowace jam'yya har kan mulkin kasar.
Ga karin bayani