Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar EFCC Na Cigaba Da Tsare 'Ya'yan Gwamna Lamido


Gwamnan Sule Lamido na Jihar Jigawa
Gwamnan Sule Lamido na Jihar Jigawa

Yayin da dambarwar jam'iyyar PDP ke kara tsamari sai gashi hukumar EFCC ta kame 'ya'yan Gwamna Lamido, daya daga cikin gwamnonin da suka yiwa PDP tawaye.

Yayin da rikicin PDP ke kara ruruwa sai gashi hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kame 'ya'yan Sule Lamido gwamnan jihar Jigawa, daya daga cikin gwamnonin dake yiwa jam'iyyar tawaye.

Kawo yanzu hukumar EFCC tana cigaba da tsare Aminu da Mustapha 'ya'yan Gwamna Sule Lamido kan zargin yin badakala da nera miliyan dubu goma ko N10bn a takaice. Ita hukumar bata nuna alamun gurfanar dasu yau Litinin ko wata rana a gaban kotu ba. Jami'in labarun hukumar ya ce har yanzu ana yi masu tambayoyi. Gurfanar dasu gaban kotu ya dangantaka ga masu bincike da irin amsoshin da Aminu da Mustapha suka bayar.

Sakataren karamar hukumar Maigatari ta jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar ya ce wannan bita da kullin siyasa ne. Ya ce siyasa irin ta burga ba zata kai kasar inda ake zato ba. Ya ce irin su Gwamna Lamido su ne suka kafa jam'iyyar PDP su ne kuma suka kori soja daga milkin kasar har yau kowa yake walwala ya samu damar fadan albarkacin bakinsa. Duk dimokradiyan da a keyi su ne kashin bayanta. Ya ce shi bai yadda zasu ce ta irin wannan hanyar za'a iya cin Gwamna Lamido da yaki.

Wani shahararren matashin adawa daga Jigawa Ibrahim Musa ya garzaya zuwa ofishin Muryar Amurka a Abuja inda ya ce gwamnatin Jonathan na nuna banbanci a yaki da cin hanci da rashawa. Ya yi misali da ministar ma'aikatar zirga zirgan jiragen sama wadda ta shiga cikin wata barna da kudaden kasa inda 'yan kabilarta suka fito da yin zanga-zangar kada a tabata ko a koreta daga mukaminta. Sun ce idan an tabata duniya zata tashi. Malam Musa ya ce to idan wariya za'a nuna a kan yaki da cin hanci to zasu yi fito na fito da gwamnati tarayya sai dai idan ta hukunta kowa da kowa.

A kan tsohon gwamna Ibori, Ibrahim ya ce kotun Najeriya ta wankeshi sai da ya fita zuwa kasar waje aka sameshi da laifi. Ya ce ba kotun Najeriya ba ce ta daureshi. Kotun Ingila ce ta yi aikinta.Da a Najeriya yake da ba za'a hukuntashi ba. Ya ce kuma tsohon gwamnan Bayelsa da wasu yafe masu aka yi kuma har lambar yabo aka basu.

Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG