A Najeriya ma kowane gwamna na iyakacin bakin kokarinsa ya inganta ilimi a jiharsa da tabbatar da cewa an samarda ilimin cikin sauki kuma mai inganci.
Jihar Jigawa ita ma ba'a barta a baya ba a harkokin ilimi. Wakilin Muryar Amurka Ladan Ibrahim Ayawa ya leka daya daga cikin makarantun jihar dake garin Bamaina a cikin karamar hukumar Birnin Kudu. Bayan samarda kyakkyawan muhalli a makarantar daliban kuma suna nan pes-pes.
Wani malami Dahiru Uba dake aiki a makarantar ya bayyana yadda dalibai ke shigowa makarantar. Kafin a dauki yaro sai ya zama shi ne mafi kwarewa a makarantarsa ta baya kana ya zo yayi jarabawa a karamar hukumarsa. Bayan hakan zai zo makarantar ya sake yin jarabawa. Idan ya ci sai a daukeshi.
Kusan duka azuzuwan makarantar kujeru basu da yawa. Na yara ashirin ne kawai, ma'ana babu ajin da yake fiye da dalibai ashirin sai ajin farko dake da ashirin da biyar. Kuma duk malamin dake koyaswa a makarantar yana samun alawus na musamman kashi talatin akan albashin da yake karba.
Wasu dalibai da aka zanta dasu sun bayyana abun da suke so su zama. Wata Aisha tace ita tana son ta zama likita domin ta taimaki kasarta. Shi ma Aliyu yace yana son ya zama injiniya mai kere-kere domin ya kera kamar mota ko jirgin sama.
Bayan wannan makarantar tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo ya dauki wata makarantar da yace shi ne zai dauki nauyinta na komi da komi.
Gwamnan jihar Alhaji Sule Lamido yace gwamnatin jiharsa ta zarta mizanun adadin abun da hukumar samarda ilimi ta majalisar dinkin duniya tace a samar a matakin gwamnati.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.