Kungiyoyi da dai-daikun mutane na nuna sha’awarsu akan tsayawar gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido takarar shugaban kasa duk da cewa shi gwamnan bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zabe mai zuwa ba.
Amma matakin da gwamnan ya dauka na kin halartar taron PDP da aka yi a Kaduna, da watsi da kudirin da aka cimma na amincewa da shugaba Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, wata manuniya ce da ke nuna cewa ta yiwu gwamnan ya amsa kiran da wasu ‘yan Najeriya ke yi masa.
Alhaji Sale Taki tsohon shugaban karamar hukuma a jihar ta Jigawa, yace jinkirin da gwamnan ke yi na bayyana aniyarsa akwai hikima a ciki. Don a ta bakin sa, in ka ga mutum na saurin neman kujera kafin lokaci yayi, ba kwararre bane kuma bai san siyasa ba. Ya kara da cewa gwamana Sule Lamido shine zai shugabanci Najeriya ba tare da nuna banbancin kabila ba.
Shima kamar Sule Lamido, shugaba Goodluck Jonathan har yanzu bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa ba, shin ko mai hakan ke nufi a fagen siyasar Najeriya?
Wani mai fashin baki akan lamuran demokradiyya kuma Darektan Nazarin cibiyar demokradiyya ta kasa-da-kasa Mallam Abbati Bako, yace bisa tsari, dole ne a yi bincike da tuntubar shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a kasa baki daya, da kamfanoni, da kuma kasashen da ke da sha’awa akan Najeriya. Ta yiwu shugaba Jonathan na jiran rahoton kididdigar binciken ne akan abinda zai iya faruwa kafin ya bayyana ra’ayinsa.
Wakazalika shima Sule Lamido, ta yiwu yana jiran sakamakon masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ne don ya ga wa zasu mara ma baya tsakanin sa da shugaba Jonathan. Wakilin muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari a Kano shine ya bada wannan rahoton kamar yadda za ku ji a nan.