Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Lamido Ya Taya Buhari Murna


Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido.
Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido.

Yayinda yake ganawa da manema labarai a Dutse fadar gwamnatin jihar Jigawa, gwamna Sule Lamido ya yabawa Janar Buhari.

Gwamnan ya yaba da kalamun dattaku da suka fito daga shugaba Janar Buhari mai jiran gado.

Yace an yi zabe lafiya an kuma gama lafiya kalau. Banda haka yace shugaban kasa mai barin gado, Goodluck Jonathan, ya yi karamci da ya yadda cewa ya fadi ya kuma taya Buhari murna. Matakan da shugabannin suka dauka sun taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a kasar.

Yace kullum maganar Najeriya a keyi ba ta bangaranci ba. Ya godewa Allah cewa kasar ta tsallake siradin wargajewa kamar yadda wasu suka yi harsashe da can.

Gwamnan na Jigawa yace daya daga cikin abubuwan da suka kaifafa siradin da Najeriya ta tsallake shi ne zafafan kalamai da suka dinga fitowa daga bakunan masu neman madafin iko a yayin yakin neman zabe. Gwamna yace an samu zafafan kalamu yawancinsu na karya lamarin da ka iya dawowa ya zama kalubale ga shugabancin Najeriya. Yayi fatan 'yan Najeriya zasu daukaka da'arsu ta 'yan kasa fiye da addinsu ko kabilarsu ko jinsi. Ya kamata 'yan kasar su soma girmama hakin kowa ba tare da nuna banbanci ba na kowane iri.

Gwamna Lamido ya yi fatan cewa alamura zasu kyautata da zasu kai ga karfafa dimokradiyar Najeriya ta mike sosai. Wasu abubuwa na siyasa suna bukatar hakuri da dauriya da jajircewa da sadakarwa da kuma rashin tsoron fadin gaskiya.

Wakazalika gwamnan yace nasarar gwamnatin da Buhari zai kafa zata ta'allaka ne akan irin taimakon da 'yan Najeriya zasu bashi. Yace zaben da aka yi ya gamu da fushin 'yan Najeriya ne sabili da haka zasu sa ido su bi sawun duk abun da gwamnatin zata yi. 'Yan Najeriya sun san cewa ana zalunci ta koina. 'Yan Najeriya suna son Buhari yayi maganin komi a Najeriya to amma bashi da wannan halin. Ya zama dole 'yan Najeriya din su bashi gudummawa tare da yin hakuri. Dan Najeriya yana son komi a yi masa yanzu. Buhari ya ci zabe saboda haka komi zai daidaitu nan da nan.

Idan an gama yin murna lokaci na zuwa da za'a fuskanci shugabanci na 'yan Najeriya gaba daya. Buhari ba shugaban kasar musulmi ba ne ko kasar kirista ko na Fulani ko Hausawa ko na Angas. Idan ana son a yi nasara dole a daina yin wasu abubuwa na gadan-gadan na nuna banbanci. Dole sai an binnesu domin kada a sa sauran kabilu su yi fushi. Wajibi ne. Yace ya san burin 'yan Najeriya musamman 'yan arewa shi ne sha yanzu magani yanzu, wato a biya masu bukatunsu ba tare da la'akari da hakin sauran 'yan kasan ba.

Ga rahoton Ibrahim Mahmud Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG