Majalisa ta Kira Shugaban Sojoji Akan Cibok

Daya daga cikin iyayen Cibok tana zubar da hawaye a gaban Majalisar Kasa, a birnin Abuja dake Najeriya.

Majalisar kasa ta ce Gwamnatin Tarraiyya ta samo yan matan nan da yan ta'adda suka sace ko suna da rai ko babu.
'Yan majalisar sunyi wannan furuci ne bayan zaman da suka yi akan batun tsaro, biyo bayan zanga-zangar da wasu mata 'yan Cibok suka yi a harabar majalisar.

Senata Zainab Kure, ‘yar majalisar dattawa ce “bamu ji dadi ba baki daya, da abunda ya faru. Na biyu, mun nuna tausayinmu ga iyaye, da dalibannan da kuma gwamnatin Borno”.

A halin yanzu dai, majalisar wakilai tace tana bukatar shugaban rundunar sojoji ya gurfana a gabanta nan bada jimawa ba, domin yayi bayanin matakan da ake dauka wajen gani an kubuto da daliban.

Hukumar tsaron Najeriya, ta bakin kakakinta Chris Olukolade ta fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban, kalamun da iyaye da hukumomin makaranta suka musanta, kuma daga baya hukumar tsaron ta janye kalamunta. Ya zuwa yanzu dai bata sake bayanna wani mataki ko daya ba, akan irin aikin da takeyi na gani ta ceto daliban.

Shugaba Jonathan a baya-bayannan ya gudanar da taro da duka gwamnoni, da shuwagabannin al-umma, da hukumomin tsaro game da batun tsaro, inda taron ya kayyade da bayanna matakai da za'a dauka domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Daliban mata su 234, ‘yan ajin karshe ne dake rubuta Jarrabawar Fita daga Sakandare a Yammacin Afirka, ko WAEC a takaice a lokacin da ‘yan bindiga suka kaiwa makarantarsu farmaki cikin daren Litinin, sama da makonni biyu kennan, inda suka kona makarantar mallakar gwamnati baki dayanta, sannan suka kwashe daliban a cikin manyan motoci suka tafi dasu.

Gwamnatin Jihar Borno tayi alkawarin bada tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada wani bayani da zai kai ga ceto yaran mata.

A baya-bayannan ma, Gwamnan daya daga cikin jihohin dake da dokar-ta-baci, wato Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya zargi da hannun gwamnati a rincabewar lamuran tsaro a arewarin Najeriya, zargin da gwamnati ta musanta, kuma wasu shuwagabanni a Najeriya da dama suka yi ta sukan gwamna Nyakon. Har yanzu tsohon hafsin rundunar sojin ruwa bai janye kalamunsa ba, wanda a ciki harda tattara shaidu na kaiwa kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa a birnin Hague, domin tuhumar Shugaba Jonathan da kisan kare dangi.

Jihar Borno dai na daya daga cikin jihohin dake fama da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, inda ‘yan bindigar nan da aka fi sani da Boko Haram suke da karfi, wadanda suka fara tayar da kayar baya tun shekara ta 2009. Ya zuwa yanzu gwamnatin Najeriya tace zata shawo kan matsalar, amma kashe-kashen mutane da kone-kone bai tsaya ba.

A kwanakin baya, 'yan siyasa sun bayanna cewa Shugaba Jonathan na so ya sabonta dokar-ta-baci, amma 'yan majalisar na daura dammarar adawa da hakan.

Your browser doesn’t support HTML5

Matan Cibok Sun Je Majalisar Tarayya - 3'32"