Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuwar 'Yan Gudun Hijira dake Borno Na cikin Mawuyacin Hali-Fafasa Al'Amin


Wasu cikin 'yan gudun hijira dake Borno
Wasu cikin 'yan gudun hijira dake Borno

Farfasa Muhammad Al'Amin shugaban hukumar samarda gidaje dake Abuja yace rayuwar 'ayn gudun hijira dake tsugune a sansanoni daban daban na cikin mawuyacin hali.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci jihar Borno saboda gani da idanunsa halin da 'yan gudun hijiran ke ciki.

Farfsa Al'Amin ya kwana a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijiran inda suke tsugune cikin garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

Farfasa Al'Amin yace ya ji ya kuma gani irin yadda 'yan gudun hijiran ke gudanar da rayuwarsu a sansanonin duk da cewa gwamnatin tarayya na kokari. Yace akwai bukatar a kara tallafawa 'yan gudun hijiran da suka samu kansu cikin wannan mawuyacin hali sakamakon rikicin Boko Haram da ya rabasu da garuruwansu.

Farfasa Al'Amin yace ya fahimci cewa akwai matsaloli wurin kwana da ruwan sha da kuma wurin zagayawa. Yace ana karancin wadannan abubuwa saboda haka ya kwana cikin daya domin shi ma ya fuskanci abun da 'yan gudun hijiran ke fuskanta kullum.

Yace rayuwarsu ba za'a ce komi ba saidai a yi addu'a Allah ya gaggauta lokacin da zasu koma garuruwansu saboda duk da taimakon da hukumar bada agajin gaggawa take yi da wasu hukumomi har da na kasashen waje amma akwai matsaloli da dama. A rumfar da ya kwana shi kadai ne amma cikin irinta kusan mutane goma ne ciki wato kowane mutum yana kwana a takure ne domin wurin da yake dashi bai fi kafa biyu ba.

Farfasa yace ya kwana a sansanin amma ya kasa anfani da mazagayarsu saboda halin da take ciki. Wurin da ake dafa masu abinci bashi da tsafta ko kadan.

Saboda zafi yace bai iya barci ba dalili ke nan da ya zagaya da dare inda ya ga wasu suna kwana kan karfen gado babu katifa. Wasu ma gadajen na waje ne dare da rana ko kuma an yi ruwa nan suke kwana.

Akan irin tallafin da yakamata gwamnati ta bayar tunda ya kwana a wurin, Farfasa Al' Amin yace 'yan gudun hijiran suna ran shugaban kasa to amma sai an kammala fatattakar 'yan ta'adan a kawar da abun da ya korosu kana a mayardasu garuruwansu.

To saidai Farfasa Al'Amin yace hukumarsa ta fito da wani sabon tsari na soma gina gidaje masu saukin kudi da kuma ginasu cikin dan karamin lokaci. Za'a iya kammala ginin gida mai dakuna uku ko hudu cikin kwana biyar kacal. Wannan wata fasaha ce daga kasar China wadda yanzu suna koyawa mutane.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG