Tashin bamabaman ya hallaka mutane da dama tare da raunata wasu.
Wannan tashin bamabaman ya auku ne kasa da makwanni biyu bayan tashin wasu bamabamai a anguwar Atilari wadanda suke makwaftaka ta juna.
Tashin bam din ya faru ne misalin karfe bakwai zuwa takwas na dare a wasu wurare daban daban. Mazauna anguwar sun shaida cewa wasu 'yan kunar bakin wake ne suka dinga kutsawa cikin jama'a suna tada bamabaman.
Amma hukumomin tsaro sun samu nasarar gano wasu daga cikin 'yan kunar bakin waken suka kuma bindigesu kana daga bisani bam din ya dinga tashi a jikinsu.
Ganao sun ce 'yan kunar bakin waken sun shigo da yawa har sun samu sun je gidan shugaban 'yan kato da gora ko 'civilian JTF" dake taimakawa jami'an tsaro wajen farautar 'yan ta'adan.
Bamabamai hudu suka tashi lamarin da yasa jama'ar anguwar da jami'an tsaro suna bi gida gida saboda tsamo wadanda ba'a sansu a anguwar ba a fitar dasu. Jami'an tsaro sun kunce wasu bamabaman da dama daga wadanda suka zakulo cikin jama'a.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.