Mayakan kungiyar Boko Haram sun sake salon yakin sunkuru da suke yi.
Yanzu suna kai harin sari ka noke a kauyukan da babu jam'an tsaro cikin jihar Adamawa.
A karamar hukumar Madagali 'yan Boko Haram sun kai har kauyuka, sun hallaka mutane kuma sun yi awan gaba da wasu. Lamarin ya razana al'ummar da suka fara komawa yankinsu daga gudun hijira.
Wani shugaban al'umma da ya nemi a kare sunansa yace da safe misalin karfe shida 'yan Boko Haram suka afkawa wasu 'yanbanga a Sabongari dake cikin karamar hukumar Madagali. Sun kashe mutane bakwai. Kana da yamma sun je kusa da Sabongarin sun kone gidaje sun kuma yi gaba da maianguwan.
Kazalika 'yanbindingan suna kai hari a kauyukan dake kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru ta yankin jihar Borno.
Babagana Malarima shugaban karamar hukumar Kalabarge yace har yanzu babu yankin karamar hukumar da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram. Amma yana fatan nan ba da jimawa ba sojoji zasu kai yankin nasa. Rashin hanya ya sasu cikin halin da suka shiga.
'Yan Boko Haram suna mugun barna a karamar hukumar Kalabargen. Suna kashe kashe da sace sace.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.