Bamabaman sun yi sanadiyar mutuwar mutane hamsin da hudu mutane fiye da saba'in ne kuma suka jikata.
Gwamnan ya zagaya unguwannin da bamabaman suka tashi inda ya yiwa jama'a jaje da kuma yiwa wadanda suka rasa 'yanuwa ta'a ziya.
Gwamnan ya je asibitin Umaru Shehu inda ya ga masu jinya sakamakon raunukan da suka samu daga tashin bamabaman. Nan take gwamnan ya yi alkawarin biyan kudin jinyarsu.
Gwamnan yace ya ji takaicin abun da ya faru amma da yaddan Allah irin wannan haukar ta zo karshe saboda kudurin shugaban kasa na ganin an dakile ta'adanci..
Gwamna Shettima ya gargadi jama'a da su shaidawa jami'an tsaro da zara sun ga wanda basu yadda dashi ba.
Ga karin bayani.