Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maiduguri: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu


Boko Haram
Boko Haram

Bayanai daga Jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa ana samun karuwar yawan mutanen da suka mutu a hare-haren bam da aka kai a birnin Maiduguri.

Rahotanni daga birnin Maiduguri da ke Jahar Bornon Najeriya na cewa adadin mutanen da suka mutu a hare-haren bam din da aka kai a jiya Lahadi ya kai 56.

Bayanan da aka samu bayan kai harin sun nuna cewa mutane 54 ne suka mutu a wurare hudu da aka jefa bama-baman.

A jiya Lahadi aka kai hare-hare a masallacin da ke Ajilari da Ajilari tsallake da wani wuri da ake cajin waya da kuma wani gidan kallo da ke unguwar Gomari.

Wasu mazauna unguwannin da aka kai hare-haren sun ce bam din da aka saka a masallaci ne ya fara tashi kana sauran na wuraren suka amsa.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare-hare, amma irin wannan hari na da nasaba da irin wanda aka san kungiyar Boko Haram da kaiwa.

Ga karin bayani a wannan rahoto na Haruna Dauda Biu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG